Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP
Published: May 9, 2026 at 10:37 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Gombe tare da haɗin gwiwar Asusun Tallafin Duniya na Global Fund da Hukumar Yaƙi da Cutar Kanjamau ta Ƙasa, NACA, sun ƙaddamar da maganin rigakafin kamuwa da cutar HIV mai suna LENACAPAVIR ko kuma LEN PrEP, wanda ake yi wa mutum allura sau biyu kacal a shekara.

An tsara wannan magani ne domin mutanen da ba su ɗauke da cutar HIV ba, musamman masu shiga haɗarin kamuwa da cutar, domin hana yaduwar sabbin kamuwa da cutar.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da maganin, Babban Sakataren Hukumar Raya Kiwon Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Gombe, Dakta Abdurrahman Shu’aibu, ya ce hukumar za ta horas da ma’aikatan lafiya tare da ƙara sa ido da wayar da kan jama’a a matakin ƙasa domin kawar da jita-jita da rashin fahimta dangane da sabon maganin allurar.

Dakta Shu’aibu ya bayyana cewa jihar Gombe ita ce jiha ta takwas da aka zaɓa domin fara amfani da maganin rigakafin HIV ta allura, yana mai danganta hakan da irin ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen bunƙasa harkokin lafiya.

Shi ma Daraktan Kula da Cututtuka na Hukumar Raya Kiwon Lafiya ta Matakin Farko ta jihar, Dakta Mustafa Musa, ya ce maganin yana da inganci kuma an tanade shi ne domin mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar HIV, domin rage yaɗuwar cutar.

A nasa jawabin, Manajan Shirin Kula da Cutar Hepatitis da Cututtukan Saduwa ta Jihar, SASCP Mohammed Sanusi, ya bayyana maganin a matsayin wani muhimmin ƙari a dabarun rigakafin HIV a jihar.

Ya ce an riga an samar da maganin a cibiyoyin lafiya da aka ware, ciki har da Asibitin Kwararru na jihar Gombe da Babban Asibitin Kaltungo, tare da kira ga waɗanda suka cancanta da su yi amfani da damar.

Taron ƙaddamarwar ya haɗa da yi wa wasu da suka amfana allurar rigakafin HIV da kuma sauran ayyuka masu alaƙa da wayar da kai

Afrika, Kimiya, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato
Next Post: Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
Birtaniya Zata Fara Raba Rigakafin Allurar Cutar Sankara Kimiya
Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika
Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
  • Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
  • Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
  • Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC Siyasa
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Najeriya
  • Ko Meye Gaskiyar Rade-Radin Zanga-Zanga A Jos Dake Jihar Filato Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.