Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU Afrika
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja Afrika
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya Afrika
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya Afrika
  • Afirka Na Bukatar Adalci Da Tallafin Kuɗi Wajen Yaƙi Da Sauyin Yanayi – ACR Afrika

KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli
Published: November 4, 2026 at 5:34 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: November 4, 2026

Ƙungiyar Kaduna State Climate Change Accountability Mechanism (KADCCAM) ta yi kira ga mafarauta, manoma, ’yan kasuwa da sauran al’ummar Jihar Kaduna da su guji kona dazuzzuka ba bisa ƙa’ida ba, tare da ɗaukar matakan kariya daga tashin gobara yayin da lokacin hunturu (Harmattan) ke gabatowa.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa yanayin lokacin Harmattan, wanda ke tattare da bushewar ciyayi, ƙarancin danshi a iska, iskar ƙura da tsananin bushewa, na iya haifar da saurin yaɗuwar gobara a unguwanni, kasuwanni, gonaki, dazuzzuka da sauran wuraren da ke da rauni.

A cikin wata sanarwa, Mataimakin Daraktan ƙungiyar KADCCAM, Ibrahima Yakubu, ya shawarci mafarauta musamman da su daina cinna wa dazuzzuka wuta yayin farauta, yana mai gargaɗin cewa irin wannan ɗabi’a na iya haddasa mummunar gobara, lalata ciyayi da bishiyoyi, hallaka namun daji tare da jefa al’ummomin da ke kusa cikin haɗari.

Ya kuma shawarci manoma, iyalai, ’yan kasuwa da masu kamfanoni da su riƙa taka-tsantsan wajen amfani da wuta, kayan girki, na’urorin lantarki da sauran abubuwan da ka iya haddasa gobara.

Ibrahima Yakubu ya gargaɗi al’umma kan illar kona daji ba bisa ƙa’ida ba, zubar da ragowar sigari ba tare da kulawa ba, ƙona shara a fili da kuma ajiye abubuwa masu saurin kamawa da wuta a kusa da wuraren zafi.

Ya ƙara da shawartar gidaje da cibiyoyi da su riƙa duba wayoyin lantarki a kai a kai, kashe na’urorin da ba a amfani da su, samar da kayan kashe gobara gwargwadon iko, tare da tabbatar da cewa hanyoyin shiga da fita na gaggawa suna a buɗe.

Baya ga rigakafin gobara, KADCCAM ta nuna damuwa kan wasu ayyukan da ke lalata muhalli, waɗanda ka iya ƙara ta’azzara illolin lokacin Harmattan, ciki har da zubar da shara barkatai, sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba, lalata ciyayi da kuma ayyukan da ke haifar da gurɓatar iska.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga manoma da makiyaya da su rungumi hanyoyin kula da ƙasa masu kare muhalli, da kiyaye bishiyoyi da ciyayi, tare da guje wa kona daji ba tare da kulawa ba, domin rage zaizayar ƙasa da kuma kiyaye daidaiton muhalli.

Haka kuma, ta shawarci mazauna jihar da su ɗauki matakan kariya daga ƙurar Harmattan da sauran matsalolin lafiya da muhalli, ta hanyar rage shiga wuraren da ƙura ke da yawa, kula da tsafta, kiyaye hanyoyin samun ruwa da kuma ba da kulawa ta musamman ga yara, tsofaffi da mutanen da ke fama da matsalolin numfashi.

KADCCAM ta jaddada cewa kare muhalli da hana afkuwar ibtila’in gobara nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, wanda ke buƙatar haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, sarakunan gargajiya da na addini, ƙungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin farar hula da daidaikun jama’a.

Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci mazauna jihar da su gaggauta kai rahoton duk wata gobara ko aukuwar matsalar muhalli ga hukumomin da abin ya shafa, maimakon ƙoƙarin tunkarar gobara mai haɗari ba tare da horo ko kayan aikin da suka dace ba.

A ƙarshe, KADCCAM ta yi kira ga kowane mazaunin Jihar Kaduna da ya ɗauki kare muhalli a matsayin nauyin da ya rataya a wuyansa a kullum, tana mai cewa hana gobara, kare bishiyoyi, rage gurɓatar muhalli da tsaftace unguwanni su ne muhimman matakai wajen gina Jihar Kaduna mai aminci, lafiya da kuma juriya ga sauyin yanayi.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe
Next Post: Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamna Buni Ya Gana Da Limamai, Ya Buƙaci Su Taimaka Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya Labarai
Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato Afrika
Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU
  • Jami’in NSCDC Ya Harbe Direban Tirela A Gombe
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
  • Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya Afrika
  • Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi Afrika
  • Shugaba Donald Trump Ya Bayyana Cewa Yana Cikin Masu Zaben Sabon Jagoran Iran Amurka
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yabawa ‘Yan Jarida Kiwon Lafiya
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
  • INEC Ta Amince Da Pantami Da Gwarzo Su Ci Gaba Da Takarar Gwamna Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.