Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya, NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya Abdullahi, ya jajanta wa mahukunta da ma’aikatan Gombe Media Corporation, GMC, bisa gobarar da ta lalata ginin da ke ɗauke da ɗakunan shirye-shiryen talabijin na kamfanin.
Gobarar ta afku ne ranar Asabar, inda ta haddasa asarar kayayyaki da na’urorin aikin watsa shirye-shirye da dama.
Kwamared Alhassan Yahaya, wanda yake Legas lokacin da gobarar ta faru, ya kafa tawaga ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban NUJ na Shiyya ta E, Kwamared Zare Baba, domin ziyartar GMC tare da isar da saƙon jajenta a madadinsa.
Shugaban NUJ ya ce ya karɓi labarin gobarar cikin matuƙar kaduwa, musamman ganin yawan kayayyaki da kayan aikin da suka salwanta sakamakon gobarar.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa, bisa jajircewar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, za a gyara ginin da abin ya shafa tare da maye gurbin kayan aikin da suka lalace.
Kwamared Alhassan Yahaya ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa samar da na’urorin watsa shirye-shirye na zamani da suka taimaka wajen mayar da gidajen rediyo da talabijin mallakar jihar zuwa tsarin dijital.
Ya ce ’yan jarida, musamman masu aikin jarida a Jihar Gombe, za su ci gaba da tuna irin gudunmawar da gwamnan ya bayar wajen bunƙasa harkar kafafen yaɗa labarai a jihar.
Haka kuma, Shugaban NUJ ya roƙi Gwamna Inuwa Yahaya da ya taimaka wajen kammala ginin Sakateriyar NUJ da ke Gombe tare da miƙa shi ga ’yan jarida kafin ƙarshen wa’adinsa.
Da yake mayar da martani a madadin Darakta-Janar na GMC, Dr. Ibrahim Isa, Daraktan Talla na kamfanin, Alhaji Ahmad Muhammad Ibrahim, ya gode wa Shugaban NUJ bisa wannan ziyara da nuna kulawa.
Ya kuma yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ci gaba da tallafa wa Gombe Media Corporation da kuma ƙoƙarin inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai na jihar.


