
Yayin da albarusan sojojin Isra’ila ke dira a kan al’ummar Gaza a gefe guda kuma yunwa na ragargazar mazauna yankin. Kimanin mata da yara dubu 100 ke fama da mawuyacin yanayi na karancin abinci. Babban jami’in hukumar samar da abinci da duniya Ross Smith ya ce Gaza na gab da aukawa mummunan yanayin karancin abinci ko kai tsaye a ce yunwa. Smith ya ce baa bun da ke tafiya a Gaza don ba batun kasuwanni ko a ce wata hada-hada ga shi an takaita hanyoyin isar da kayan agaji. A nan jami’in ya nuna hakika abun da a ke bukata shi ne bude hanyoyin kan iyaka don shigowar kayan abinci da samun amincewa na jami’an tsaro wajen raba abincin. Al’ummar Gaza na cikin yanayi na rashin tabbas dare da rana don koyaushe wani bom zai iya fadowa ya hallaka su. Ba batun jinya asibiti ko zama a tantunan gudun hijira, sammakal ko ina sojojin Isra’ila ka iya kai harin su wa imam ta jiragen yaki ko motocin yaki ta doron kasa. A iya nuna nadamar kasha wadanda ba su yi laifin komai ba, Isra’ila kan ce kuskure ko za ta gudanar da bincike. Idan kuskure ne me ke kawo maimaita kuskure a kusan kowane lokaci? In kuma bincike a ke yi ina sakamakon binciken? In an samu wasu masu zarmiya wane hukunci a kan dauka a kan su? Akwai fa lokacin da wasu sojojin Isra’ila su ka nuna yakin nan na Gaza ya isa hakanan zubar da jinin ya yi yawa. Sakamakon wadannan sojojin shi ne sallama daga aiki. Ita dai gwamnatin Netanyahu ta shahara wajen ina da yaki ko kai hare-hare na kashe duk wanda ya dagawa kasar yatsa. Idan a na maganar Falasdinawa duk neman zaman lafiyar su ai ba za su cigaba da zama bayi a kasar su ta gado ba. Kai a je ma kawai Falasdinawa sun zauna babu gwagwarmayar Hamas, ba yanda za a yi Isra’ila ba ta rika cafke matasa ta na zargin su da cewa su na da niyyar kai hari kan muradun Isra’ila. An sha harbe matasa Falasdinawa kan wani zargi da bai kai ya kawo ba. Idan an kashe Bafalasdine tamkar an kasha dan ta’adda ne ba wani mataki ko tausayi da za a ji. Gaskiya jinin Falasdinawa fa ya zama kamar na kiyashi don yawan shekarun da a ka yi a na kisan gilla gare su tun wajen 1948 na nuna ba a dauke su da daraja ba ko ma dai a ce dama a na son kwace kasar su ne da karfin tuwo. Duk wani labara na Falasdinawa da za ka gani ya shafi kisa ne na mata da kananan yara ko daure wani matashi har ya tsufa a gidan yarin Isra’ila. Kazalika duk wanda ya fito da sunan shi dan kungiyar Hamas ne to an yanke ma sa hukuncin kisa sai jiran lokacin zartarwa. Me manufar Hamas kuma me ya sa a ka kafa kungiyar daga marigayi Ahmad Yasin da a ka kashe kan keken sa na guragu lokacin tafiya sallar asuba? Ko me za mu ce kungiyar ta gwagwarmayar kwato hakkin Falasdinawa ne da a ka danne ta hanyar hana su kasar su inda duk wani batu da ya shafi a ba da dama kamar raba kasar biyu Isra’ila ta dau bangare daya Falasadinawa su dau daya bangaren na samun watsi daga Isra’ila. Abun da Isra’ila ke so ko dai Falasdinawa su bar yankin su yi gudun hijira a wasu kasashen Larabawa ko kuma su rika zama kamar bayi a yankunan da su ke rakube. Gwamnatin Falasdinawa ta birnin Ramallah karkashin Mahmoud Abbas na irin wannan zama na nuna takaici da baki kan muzgunawar Isra’ila amma ba daga kara. Sau nawa a na batun kafa kasar Falasdinu mai babban birni a gabashin birnin Kudus amma hakan ya kasa tabbata. Kun ga ko majalisar dinkin duniya irin wannan yanayi ta ke samun kan ta a ciki sai dai nuna takaici don da zarar an zo daukar mataki mai tsauri, Amurka za ta hau kujerar na ki shikenan magana sai ta shiririce. Kasashen Larabawa ba su da babban matakin da za su dauka don yanayin kalubalen siyasar duniya mai bukatar sara da duba bakin gatari don yanyin akasarin su na mulkin mulukiyya. Hakika da zarar kasashen Larabawa masu aiki da tsarin sarauta sun nace lallai sai Falasdinawa sun samu ‘yanci, kasashen yamma ka iya kunno mu su wutar su koma tsarin dimokradiyya. Mu tuna kuma abun da ya faru ga marigayi shugaban Masar Muhammad Morsi wanda ya bude mashigar Rafah don samawa Falasdinawa sararawa sai kawai a ka kunno ma sa fitina har a ka kifar da gwamnatin sa a dan kankanin lokaci da ma karshe ya rasa ran sa gaba daya. Manyan kasashe sun mara baya ga gwamnatin soja ta Alsisi da ta amshi madafun iko ta watsar da ta Morsi wacce ta lashe zabe ta hanyar dimokradiyya. Shawara ga Falasdinawa su kara dagewa ga addu’a don neman taimakon Allah ya yaye mu su wannan fitina da ke daukar rayukan su ba yaro ba babba. Mutuwa dai ba bakuwar aba ba ce a tsakanin Falasdinawa kuma iyaye ma mata kan rungumi gawar ‘ya’yan su, su yi kuka inda su din ma wani lokacin makamin ya dira a kan su. Ina yabawa wasu jakadun Falasdinawa da ke kokarin fahimtar da duniya asalin abun da ke faruwa a Gaza ko ma kasar ta Falasdinawa sabanin yanda a ke nuna ‘yan ta’adda a ke yaka. Kazalika da ganar da duniya wadanda a ke kashewa a Falasdinu ba musulmi ba ne kadai har da mabiya addinin kirista. A na samun wasu mabiya addinin kirista da ba sa damuwa da ‘yan uwan su Falasdinawa inda ido rufe su ke marawa Isra’ila baya. Tamkar ma bai cancanta a samu Bafalasdine ya zama kirista ba. Isra’ila dai kan kai hari kan kowa ba rowan ta da kowaye matukar ya na yankin Falasdinu ko ya na gwagwarmayar tabbatar da kafa kasar Falasdinawa. Amfani da jiragen yaki wajen kai hari ga wadanda ke yawo ko key akin sari ka noke a yankin su na nuna amfani da karfi marar kima da kan kare kan mata da kananan yara.