’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta ce ta samu gagarumar nasara a ayyukan da take gudanarwa na yaƙi da garkuwa da mutane, ’yan bindiga, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a faɗin jihar. Rundunar ta ce a ranar 8 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe takwas na safe, jami’an ’yan sanda, sojoji, Hukumar Tsaron Fararen…

