Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
Published: July 25, 2026 at 4:51 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa maboyarsu a wasu sabbin hare-hare da suka kai ta sama da ƙasa a jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Hare-haren da aka gudanar ƙarƙashin Operation HADIN KAI da Operation FANSAN YAMMA sun kuma haifar da ceto waɗanda aka sace, kama masu garkuwa da mutane da kuma ƙwato makamai da sauran kayayyakin sadarwa.

A Jihar Borno, dakarun Bataliya ta 212 sun kama wani da ake zargin ɗan ƙungiyar ISWAP ne a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno, inda aka same shi da na’urar Starlink, na’urar Wi-Fi mai tashoshi shida, wayar salula da kuɗi.

Haka kuma, dakarun Bataliya ta 82 sun ceto wasu ‘yan mata biyu a yankin Gwoza, waɗanda suka bayyana cewa an sace su tun watan Agustan 2025 a kan hanyar Pulka zuwa Ngoshe, kuma suka tsere daga sansanin ‘yan ta’adda da ke Dutsen hMandara.

A Jihar Yobe kuwa, dakarun Brigade ta 27 sun daƙile wani harin dare da ‘yan ta’adda suka kai wani wurin binciken sojoji a hanyar Buni Yadi zuwa Buni Gari da ke ƙaramar hukumar Gujba. Sai dai sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin fafatawar, yayin da aka lalata motar yaƙi ta ‘yan ta’addan.

A wani samame kuma, dakarun Bataliya ta 233 tare da haɗin gwiwar mafarauta sun kama mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Jegalari na ƙaramar hukumar Fune, inda aka ƙwato bindigogi, alburusai da wayoyin hannu.

Rahoton ya ce hare-haren sama da aka kai bisa bayanan sirri sun yi mummunar illa ga ‘yan ta’adda. A yankin Kala Balia da ke ƙaramar hukumar Marte ta Borno, jiragen yaƙin sama sun kashe kusan ‘yan ta’adda 15 bayan an gano maboyarsu.

Haka kuma, a wani harin dare da aka kai tsakanin Bama da Maiduguri, an kashe wasu ‘yan ta’adda takwas bayan jiragen yaƙi sun yi luguden wuta kan wuraren da aka gano motsinsu.

A Arewa maso Yamma, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun fafata da ‘yan ta’adda a Dutsen Gambada da ke ƙaramar hukumar Gummi ta Jihar Zamfara.

Haka kuma, dakarun Brigade ta 12 sun hana wani yunƙurin satar mutane a kan hanyar Kabba zuwa Ayere a Jihar Kogi tare da ceto mutum shida da aka sace, waɗanda aka kai Asibitin St. Joseph da ke Kabba domin kula da lafiyarsu. A Jihar Nasarawa ma, dakarun Operation WHIRL STROKE sun ceto wani da aka yi garkuwa da shi a yankin Tunga na ƙaramar hukumar Awe.

A Kudu maso Gabas kuwa, dakarun Operation UDO KA sun kai samame wani maboyar masu aikata laifuka a yankin Awara Waterside, inda suka ƙwato bindigogin Lee-Enfield da G3 tare da alburusai masu yawa. Rundunar Sojin Najeriya ta ce waɗannan nasarori sun nuna cewa ana ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane lamba ta hanyar amfani da ingantattun bayanan sirri da haɗin gwiwar hare-haren sama da ƙasa, tare da jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi har sai an kawar da dukkan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
Next Post: NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis

Karin Labarai Masu Alaka

Prime Ministan Pakistan Yace Zai Karbi Bakoncin Tattaunawar Amurka Da Iran Afrika
Akwai Doka Mai Tsanani Wajen Mallakar Bindiga A Kasashen Yammacin Turai Labarai
Najeriya, Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto 34 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
Amurka Tafara Mayar Da ‘Yan Afghanistan Da Suka Makale A Qatar Amurka
Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
  • Sanata Barau Ya Raba Motoci Da Babura Ga Al’ummar Kano Ta Arewa Afrika
  • An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
  • Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • Birtaniya Ta Bukaci Israela Ta Janye Shawarar Fadada Iko Da Kogin Jordan Labarai
  • Rundunar Sojin Amurka Zasu Kaiwa Iran Hari Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.