Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Yunkurin Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi Na Kara Kankama A Najeriya
Published: March 13, 2026 at 8:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yunkurin samadda ‘yan sandan jihohi na kara kankama a Najeriya, tun bayan da sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Olatunji Disu ya kaddamar da wani komiti mai mutane takwas da zai duba yadda za’a aiwatar da ‘yan sandan jihohi a Najeriya.

Sufetan janar na ‘yan sandan wanda ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan yin garambawul da samadda ‘yan sanda jihohi, ya kuma ce ayyukan ‘yan sandan jihohin ba zai gurgunta ayyukan ‘yan sandan Najeriya ba.

Kan haka ne, Gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang shima ya kaddamar da komiti mai mutane goma sha hudu da zasu bada shawarwari kan kafa rundunar ‘yan sandan jiha don karfafa tsaro a Jihar Filato.

Gwamnan yace komitin zai yi nazari kan batun samadda ‘yan sanda a jihar bisa tsarin gwamnatin tarayya da bada shawarwari da zasu taimaka a tattaunawar da ake yi a kasa kan sauye-sauye da ake yi na samadda tsaro.

Honarabul Musa Yunusa Ayiga, tsohon mataimakin shugaban kungiyar kwadago bangaren masu samarda wutar lantarki a Najeriya yace baiwa gwamnoni damar kafa ‘yan sandan jihohi bai dace ba.

A bangare guda kuwa, Rabaran Ayuba Asheshe yace suna addu’ar Allah ya tabbatar da alheri.

Sufeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Olatunji Disu yace kiraye-kirayen da suke samu na karfafa hanyoyin tsaro a cikin kasar, shine ya sanya su daukan matakin kaddamar da komitin da ya bashi wata guda ya gabatar da rahotonsa.

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana a jihar Filato Zainab Babaji ta aiko mana rahoto

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/AUD-20260313-WA0041.mp3
Labarai

Post navigation

Previous Post: An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya
Next Post: Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran

Karin Labarai Masu Alaka

SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i Afrika
Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai
Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
  • Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
  • Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Ya Roki Rasha Ta Taimakawa Kasar Afrika
  • Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
  • An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon Afrika
  • Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Gabatar Da Gwajin Makami Mai Linzami Afrika
  • Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.