Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
Published: July 2, 2026 at 7:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hedikwatar Tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa dakarun soji sun kashe ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya 1,597, tare da kuɓutar da mutane 1,516 daga hannun masu garkuwa da mutane a cikin ayyuka 14,221 da aka gudanar tsakanin Janairu da Yunin 2026.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, wanda Group Captain Kabiru Ali ya wakilta, ya ce an gudanar da ayyukan ne ta sama, ƙasa da ruwa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya ce dakarun sun kuma kwato bindigogi 451, harsasai 16,726 da bama-bamai da na’urorin fashewa 161, lamarin da ya hana masu aikata laifuka ci gaba da gudanar da ayyukansu.

A cewarsa, an gudanar da ayyukan a jihohin Borno, Yobe, Taraba, Katsina, Kwara, Zamfara, Sokoto, Filato, Benuwe, Neja, Oyo da Kaduna.

Sojojin sun kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 412, sun kama mutum 332, sannan mutum 132 daga cikin mayaƙan ƙungiyoyin sun miƙa wuya sakamakon matsin lambar da ake musu.

Har ila yau, an lalata na’urorin fashewa 31 cikin nasara tare da gudanar da shirye-shiryen zaman lafiya 33 da wayar da kai guda 13 a faɗin ƙasa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
Next Post: Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki

Karin Labarai Masu Alaka

Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ya Ziyarci Pindiga Labarai
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
  • Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
  • Tsohon Dan-Takarar Gwamnan PDP A Gombe Ya Shiga ADC Siyasa
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora Afrika
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.