JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya
Ƙungiyar Jewel Environmental Initiative (JEI) tare da haɗin gwiwar Jami’ar Jihar Gombe (GSU), shirin ACReSAL da Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA), sun gudanar da aikin shuka itatuwa a wasu wurare a jihar Gombe domin bikin Ranar Muhalli ta Duniya ta shekarar 2026. An gudanar da aikin ne a Makarantar Firamare ta Liman Model…

