Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tsohon Minista Ngige Ya Shiga Komar EFCC
Published: December 11, 2025 at 12:59 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Chris Ngige, tsohon Ministan Kwadago, yana tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC a halin yanzu kamar yadda Majiyar Daily Trust ta rawaito.

Fred Chukwuelobe, mai taimaka wa tsohon ministan a bangaren yada labarai, ne ya tabbatar da hakan a wani bayani da ya fitar da safiyar ranar Alhamis.

Chukwuelobe ya bayyana hakikanin yanayin lamarin ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Ngige, wanda ya taɓa zama gwamnan Anambra, an yi awon gaba da shi.

“Tun cikin sa’a guda da ta gabata nake karbar wayoyi daga abokai da ‘yan jarida suna tambayar sahihancin labarin da ake yadawa cewa Mai Girma, Dr. Chris Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ministan kwadago da ayyukan yi na baya-bayan nan, ‘an yi garkuwa da shi’. Ngige yana tare da EFCC ne,  Ba wai ‘sace shi’ ko garkuwa da shi’ akayi ba,” in ji shi a wani rubutu da ya wallafa a Facebook.

Babu tabbas kan dalilin da yasa hukumar ta tsare Ngige, domin hukumar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a lokacin da ake hada wannan rahoto.

Ngige shi ne minista na biyu da ya yi aiki a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da EFCC ta kame a kwanakin nan.

Abubakar Malami, tsohon Attoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, shima yana tsare.

Malami ya bayyana cewa ana bincikensa ne kan batun dawo da “kudin Abacha”.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano
Next Post: Rundunar Tsaro Suna Cigaba Da Nasara Akan ‘Yan Ta’adda

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Yobe Ta Sake Jaddada Ƙudirin Rage Mutuwar Yara Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Mohammed Abdullahi Abubakar Ya Sayi fom Don Tsayawa Takarar kujeran Gwamnan Bauchi A APC 2027 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa Afrika
  • Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
  • Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika
  • Yanayin Yunwa Yana Kara Ta’azarra A Somaliya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
  • Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.