Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
Published: August 23, 2026 at 8:17 PM | By: Bala Hassan

Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Bayan Wasan Szoboszlai da Newcastle

Magoya bayan Liverpool sun bukaci kociyan kungiyar, Andoni Iraola, da ya yi la’akari da ajiye dan wasan tsakiya Dominik Szoboszlai a benci bayan abin da suka bayyana a matsayin daya daga cikin wasanninsa mafi muni tun bayan komawarsa kungiyar.

Liverpool ta fara kakar Premier League da canjaras 2-2 da Newcastle United a St James’ Park, a wasan farko na gasar karkashin jagorancin Iraola.

Newcastle ce ta fara cin kwallo ta hannun Anthony Elanga, kafin Cody Gakpo ya rama wa Liverpool. Joe Willock ya sake bai wa Newcastle jagora, amma a mintunan karshe Szoboszlai ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka yi wa Victor Muñoz keta a cikin fili, inda hakan ya taimaka wa Liverpool ta tashi 2-2.

Duk da cewa Szoboszlai ne ya ceci Liverpool daga shan kashi, wasu magoya bayan kungiyar sun soki yadda ya taka leda, musamman yadda ya kasa bayar da cikakken kariya a tsakiyar fili.

Wasu daga cikin magoya bayan sun bayyana cewa wasan nasa ya kasance daya daga cikin mafi munin wasanninsa a cikin  Liverpool, tare da kira ga Iraola da ya ba matashin dan wasa Trey Nyoni dama a wasannin gaba.

Masu sharhi sun kuma yi nuni da cewa Szoboszlai ya fi tasiri idan yana taka leda a matsayi na gaba a tsakiyar fili, maimakon zurfafa baya a matsayin dan wasan da ke taimakawa wajen kare gida.

A halin yanzu, ana ganin Liverpool na bukatar karin dan wasan tsakiya mai karfin kare gida domin daidaita tsarin Iraola, musamman bayan matsalolin da aka gani a tsakiyar fili yayin wasan Newcastle.

Duk da sukar da aka yi masa, Szoboszlai ya nuna muhimmancinsa ga kungiyar ta hanyar zura kwallon bugun fenariti a minti na 99, inda ya ceto Liverpool daga fara kakar bana da rashin nasara.

Wasanni

Post navigation

Previous Post: Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.

Karin Labarai Masu Alaka

Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
Al Hilal Ta Cimma Yarjejeniya Da Pedro Wasanni
Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
Janet Ce Gwarzuwar ‘Yar Wasan Mako NWFL Wasanni
Arteta, Arsenal Zata Yi Sauye-Sauye A Janairu, Wasanni
Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
  • Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugabannin Kasashen Sahel Sunyi Taro a Mali Afrika
  • Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rikicin Hakar Gwal Ya Janyo Hallaka Mutane 70 A Sudan Ta Kudu Afrika
  • Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai
  • Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.