Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi
Published: January 23, 2026 at 9:58 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rikon sakainar kashi da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki ke yi wa dokokin da suka kare hakkin yara, na daga dalilan da al’umma ke samun kanta cikin bala’o’i da rashin tabbas.

Dokokin da suka ba yara ‘yancin samun kariya daga duk wani yanayi da zai cutar da rayuwarsu ta kowace fuska, na shimfide a kundi na majalisar dinkin duniya da na nahiya da kasa da kuma jihohi.

A wani horo da majalisar dinkin duniya da hadin guiwan cibiyar dake da’awar Samar da dokoki wa al’umma, wato CISLAC da cibiyar dake kula da yara, wato SOS Children Village Nigeria, suka yi wa ‘yan jarida a Jos, an shafe kwanaki uku ana tattaunawa kan matakan kula da yara da dokokin da suka bada kariya wa yaran.

Wani lauya mai zaman kansa, Barista Dariyem Kruslat yace al’umma da hukumomi suna da gagarumin hakki na kula da yara tun daga haihuwarsu har lokacin da zasu ci gashin kansu, don daidaita rayuwarsu.

Malama Grace Solomon dake aiki a kungiyar dake kare yara, Child Protection Network tace yara ‘yan kasa da shekaru goma sha takwas ba zasu iya kare kansu ba, don haka ya wajaba manya su kare su.

Mr Solomon Adoga na cibiyar CISLAC yace ‘yan jarida na da gagarumin gudunmawa wajen bada kariya wa yara a Najeriya.

Adoga ya kara da cewa aikin ‘yan jarida bai tsaya a iyayin rahoto kan batutuwa da suka jibanci ‘yan cin yara ko hanyoyin basu kariya kadai ba, har ma da tabbatar da duk wanda keda ruwa da tsaki wajen aiwatar da dokoki da tsare-tsaren hukumomi, sun gudanar da aikinsu.

Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke a Jos Zainab Babaji tana dauke da cikekken rahoton

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/AUD-20260123-WA0085-1.mp3
Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Masu Kare Hakkin ‘Yan Gudun Hijira A Amurka Sun Mika Koke
Next Post: Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida

Karin Labarai Masu Alaka

Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
Allah Ya Yiwa Shahararren Dan Jarida Saleh Shehu Ashaka Rasuwa Labarai
Sace Ni Bai Hana Ni Bin Hanyar Jere Ba-Ali Gantsa Labarai
Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika
Amurka Zata Kara Tura Sojoji Gabas Ta Tsakiya Afrika
Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
  • Tinubu: Munsayi Jiragen Yaki Daga Wajen Amurka Amurka
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
  • Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
  • Akwai Bukatar Hukunci Mai Tsanani Ga Duk Wanda Yayi Fyade Najeriya
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
  • Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.