Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba
Published: April 17, 2026 at 7:51 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da al’ummar Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina ƙasa mai dorewa, zaman lafiya, da wadata.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar mambobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tsarin siyasa da tattalin arziƙin da suka daɗe suna dakushe ci gaban ‘yan ƙasa, yanzu ana musanya su da sabbin tsare-tsare da za su ba kowa damar cin moriyar arziƙin ƙasa. Ya kuma sha alwashin ci gaba da aiwatar da garambawul ɗin da nufin samar wa talakawa da marasa ƙarfi guraben ayyukan yi da sauƙin rayuwa.

“Kuna wakiltar lamirin al’ummar da ke son kakkabe sarƙar talauci da yanke ƙauna,” in ji shugaban sa’ilin da yake jawabi ga tawagar.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya kada su yarda da kalaman ɓata suna na ‘yan hamayya, inda ya ce idan ma ba su ganin ayyukan hanyoyi da gadoji da ake yi, to za a samar musu da gilashin gani don su gani da kyau.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, Gwamnoni da suka haɗa da na Yobe, Gombe, Kebbi, Ebonyi, Delta, Kogi, Ekiti, Benue, Taraba, Edo, da Kaduna, Tsofaffin Gwamnoni da Shugabannin Majalisa Kamar su Aminu Bello Masari, Ifeanyi Okowa, Tanko Al-Makura, da Anyim Pius Anyim.

A nasa jawabin, tsohon Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yaba wa shugaban bisa ƙarfin halin aiwatar da sauye-sauyen da wasu shugabannin na baya suka kasa yi, musamman batun cire tallafin mai da haɗe farashin canjin kuɗi.

Masari ya tabbatar wa shugaban cewa jiga-jigan siyasar shiyyar Arewa maso Yamma suna bayansa ɗari bisa ɗari, kuma za su zagaya don duba ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a shiyyar domin wayar da kan jama’a.

Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su ci gaba da isar da saƙon fatan alheri ga jama’a a matakin gundumomi da ƙauyuka, yana mai jaddada cewa “Najeriya tana hannun amintattu.”

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe
Next Post: Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna Afrika
Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika
Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
  • Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
  • ‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
  • Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20 Afrika
  • Farmakin Da Aka Kai Makarantar Mata A Iran Yayi Ajalin Yara Da Dama Afrika
  • Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.