Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
Published: July 25, 2026 at 3:49 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Aikin tsaftar muhalli na wata-wata da aka gudanar a jihar Gombe ya samu gagarumar nasara, yayin da direbobi da masu gudanar da harkokin kasuwanci suka bi umarnin gwamnati na hana zirga-zirga a lokacin gudanar da aikin.

Wakilinmu da ya zagaya tare da kwamitin sa ido na Ma’aikatar Muhalli ta jihar Gombe ya lura cewa jami’an tsaro da aka jibge a wuraren bincike da mashigai sun hana ababen hawa da babura da suka yi yunkurin karya dokar zirga-zirga ci gaba da tafiya.

A Filin Tashar Motoci ta Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park, an ga motocin haya da fasinjoji suna jira cikin natsuwa har sai da aka kammala awanni uku na aikin tsaftar kafin su ci gaba da tafiyarsu.

Da yake zantawa da wakilinmu, Manajan Kula da Zirga-zirga na Gombe Line, Kwamared Sani Yaro, ya ce kamfanin ya yi dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da cikakken bin dokokin aikin tsaftar muhalli. Ya kuma ce mahukuntan Gombe Line sun kuduri aniyar ci gaba da tabbatar da tsaftar muhalli a tashar motocin.

Wasu direbobi, masu baburan haya (Achaba) da direbobin tasi da suka yi magana da wakilinmu sun bayyana cewa sun bi umarnin gwamnati ta hanyar dakatar da zirga-zirgarsu a wuraren da jami’an tsaro suka tanada har zuwa lokacin da aka kammala aikin.

Da yake tsokaci kan aikin, Babban Sakataren Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta jihar Gombe (GOSEPA), Dakta Auwal Baba Jada, ya bayyana cewa an haramta duk wani zirga-zirgar ababen hawa a lokacin gudanar da aikin tsaftar. Ya jaddada cewa ba daidai ba ne direbobi su fito da motocinsu su tsaya a mashigai suna jiran lokacin da aikin zai kare.

Dakta Auwal Baba Jada ya yabawa al’ummar jihar bisa goyon baya da hadin kan da suka bayar, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen samun nasarar aikin.

Shi ma da yake jawabi bayan duba yadda aka gudanar da aikin, Kwamishinan Muhalli da Gandun Daji na jihar Gombe, Alhaji Yusuf L. Jalingo, ya bayyana gamsuwarsa da yadda jama’a suka bi umarnin, yana mai cewa an gudanar da aikin cikin lumana ba tare da wata matsala ba.

Wakilinmu ya kuma ruwaito cewa a yankunan Sabon Layi, Liji da Titin Gombe Bypass an samu karancin zirga-zirga da harkokin kasuwanci, inda aka hangi ‘yan kalilan daga cikin direbobin motocin dakon ruwa suna gudanar da ayyukansu.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
Next Post: An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Tsaron Teku A Libya Tafara Janye Jirgi Mai Dauke Da Iskar Gas Labarai
‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika
Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Rivers: ‘Yan Majalisa 16 Sun Canza Sheka Zuwa APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri Afrika
Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bahagon Mancha Ya Buge Bahagon Maitakwasara Da Wasun Su! Nishadi
  • Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
  • Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
  • Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland Amurka
  • Rasha Ta Gargadi Amurka Da Isra’ila Kan Harin Iran Afrika
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
  • Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.