Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka
Published: February 21, 2026 at 8:52 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: February 23, 2026

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ranar Asabar yace hukuncin da kotun kolin Amurka ta yanke ranar jumma’a akan harajin da shugaba Trump yake azawa cinikayya da Amurka, yace yana da kyau hakan, ya kasance akwai sashen gwamnati da zai iya takawa wani sashe birki, karkashin tsarin Dimokraɗiyya.

“Babu laifi idan ana da kotun koli, ma’ana akwai doka da oda,” Macron ya fada da yake amsa tambaya dangane da hukuncin da kotun kolin Amurkan ta yanke ranar jumma’a cewa matakan harajin da shugaba Trump ya dauka a baya, basa bisa doka.

Ya kara da cewa Faransa zata yi nazarin makomar sabon harajin na kashi 10 cikin dari ga dukkan kasashen duniya masu hulda da Amurka ta fuskar kasuwanci, domin inji Macron, Faransa tana son ta ci gaba da sayar da kayayyaki da take sarrafawa da suka hada da kayan amfanin gona, kayan alatu, da kwanbo, da kuma ta fuskar jiragen sama.

Yace akwai bukatar ya kasance akwai tsinkaya, inda kasashe za su sakawa juna, ba wai kawai a yi ta gaban kai wajen mu’amala da ba.

Ahalinda ake ciki kuma, dubban ‘yan Faransa ne suka yi maci a yau Asabar a birnin Lyon, inda a makon jiya aka kashe wani mai ra’ayin mazan jiya, da ake zargin ‘yan tsantsi ne suka masa duka har lahira. Lamari da yayi matukar kada ‘yan kasar.

‘Yan sanda sun bayyana damuwar macin na yau Asabar ya zama tarzoma saboda birnin na Lyon yana cike da masu ra’ayin rikau da kuma ‘yan tsantsin.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Shugaban Kasar Brazil: Yakamata Amurka Ta Gurfanar Da Shugaban Venezuela A Kotu
Next Post: Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Yoweri Musevini Ya Zamo Shugaban Uganda Na 7 Yana Da Shekaru 81 Kuma Ya Shafe Shekaru 50 A Mulki Labarai
Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya Labarai
Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
Kasar Masar Ta Dakatar Da Wasu Ayyukan Da Ake Amfani Da Man Fetur Da Diesel Labarai
Sojin Saman Najeriya Sun Lalata Sansanonin ‘Yan Ta’adda Afrika
“Yan Wasan Super Eagles Sun Karbi Alkawarin Da Gwamnati Tayi Musu AFCON 2023 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
  • Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro. Najeriya
  • Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kasar Nijar Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Afrika
  • Jami’an Shiga Da Fice A Afirka Ta Kudu Sun Tafka Badakalar Kudade Afrika
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.