Ƙungiyar “Charismatic Bishops Conference of Nigeria” (CBCN) ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.
Shugaban CBCN, Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas, shi ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a ranar Laraba a Birnin Abuja, a lokacin da ake gudanar da babban taron Synod na 2026 na CBCN da ICCABA a Majami’ar Kiristoci ta Ƙasa.
Kawas ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da bayyana shirin ta na ci gaba da mara wa shugaban ƙasar baya ta hanyar addu’a, bayar da shawarwari da kuma wayar da kai.
Ya ce: “Mun goyi bayan sa a yanzu. Mun goyi bayan sa yau, za mu goyi bayan sa gobe, kuma za mu ci gaba da goya masa baya muddin yana son kasancewa shugaban ƙasar mu.”
Ya ƙara da cewa: “Wannan gida ya amince da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.”
Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addini da su yi amfani da tasirin su wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’umma gabanin zaɓen 2027.
Ya ce: “Ci gaba da haɗa kan wannan ƙasa na buƙatar fiye da matakan gwamnati. Yana buƙatar jagoranci nagari daga dukkan ɓangarorin al’umma, ciki har da jagorancin addini.”
Idris ya yi gargaɗi kan yunƙurin nuna matsalolin tsaron Nijeriya a matsayin yaƙin addini, yana mai cewa ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun kai wa ’yan Nijeriya hare-hare ba tare da la’akari da addinin su ko asalin su ba.
“Kada a bari wani zaɓe ya sa Kirista ya juya wa Musulmi baya, ko Musulmi ya juya wa Kirista baya, ko Arewa ta juya wa Kudu baya, ko wata ƙabila ta juya wa wata baya. Nijeriya tamu ce baki ɗaya,” inji shi.
Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Tinubu, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yaba wa ma’abota cocin kan gudunmawar su ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin addini.
Ya ce: “Gwamnati tana buƙatar gudunmawar Kiristoci wajen kyautata ɗabi’a da tarbiyyar al’umma, yayin da Kiristoci suke buƙatar yanayin da zai ba su damar gudanar da ayyukan su da kyau. Fiye da komai, Nijeriya tana buƙatar mu yi aiki tare domin amfanin kowa.”


