Kwamitin Aiwatar da Fararen Takardar Kula da Filayen Kiwo a Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Dakta Ardo Chindo Abubakar, ya kai ziyarar aiki zuwa Masarautun Billiri da Pindiga domin ci gaba da wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da aiwatar da manufofin gwamnati na samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
A lokacin ziyarar a Billiri, Shugabar Ƙaramar Hukumar Billiri, Hajiya Eglah Idris, ta tarbi mambobin kwamitin tare da tabbatar musu da cikakken goyon baya da haɗin kai wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Ta roƙi kwamitin da ya yi la’akari da bai wa manoman da suka riga suka noma a cikin filayen kiwo damar girbe amfanin gonakinsu na bana kafin a fara cikakken aiwatar da dokokin, bisa amincewar hakimai da shugabannin ƙauyuka.
Da yake mayar da martani, Shugaban Kwamitin, Dakta Ardo Chindo Abubakar, tare da Daraktan Gandun Daji na Jihar Gombe, Alhaji Musa Suleiman Kumo, sun bayyana cewa wannan shawara abin maraba ne, tare da alƙawarin yin nazari a kanta yayin aiwatar da matakan gwamnati.
Dakta Ardo Chindo ya bayyana cewa kwamitin ya fuskanci ƙalubale a wasu sassan jihar sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma, amma ya jaddada aniyarsa ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A Masarautar Pindiga kuwa, Hakimin Garin Galadima, Alhaji Muhammad Kawuwa Ahmad, ya ce a wasu lokuta hukumomin gargajiya ba sa samun bayanan wasu matsaloli tun da wuri, lamarin da ke haddasa ta’azzarar rikice-rikice.
Hakimin ya buƙaci al’umma su ci gaba da zaman lafiya da juna tare da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya domin samun ci gaba.
Shi ma Shugaban Hukumar Raya Karkara ta Pindiga (LCDA), Alhaji Garba Yakubu, Walin Pindiga, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da yanayi na zaman lafiya da inganta rayuwar al’ummar jihar.
Ya kuma tabbatar wa kwamitin da cikakken goyon baya wajen aiwatar da shawarwarin Farar Takarda domin samar da mafita mai ɗorewa ga rikice-rikicen makiyaya da manoma.
A nasa jawabin, Hakimin Kolmani, Barrista Muhammad Magaji Ibrahim, ya buƙaci a ɗauki tsauraran matakai kan duk masu mamaye filayen kiwo da gandun daji ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce duk wanda aka samu da laifin sayar da filayen kiwo ko hanyoyin shanun gwamnati ya kamata a hukunta shi bisa tanadin doka domin hana sake aukuwar irin wannan matsala.
Har ila yau, Daraktan Gandun Daji, Alhaji Musa Suleiman Kumo, ya yi kira ga masu sare bishiyoyi ba tare da izini ba da su daina wannan danyen aiki, yana mai buƙatar al’ummar jihar su kasance masu bin doka tare da bai wa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya cikakken haɗin kai wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya a jihar.


