Shugaban Hukumar Raya Yankin Kudancin Gombe (Gombe South LCDA), Auwal Jauro Bapp, tare da mataimakinsa, Dalhatu Boderi, sun yaba da shirin rabon kayan tsaftar al’ada ga ‘yan mata da Alhaji Jalo Wali ya ƙaddamar. Sun bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da ya zo kan lokaci domin inganta lafiyar mata da kuma ƙarfafa ‘ya’yan mata su ci gaba da karatunsu ba tare da tangarda ba.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban LCDA ya tabbatar wa masu shirya shirin da cikakken goyon baya da haɗin kai daga hukumarsa domin tabbatar da nasarar aiwatar da wannan shiri.
A nata jawabin, Shugabar Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Jauro Tudun Wada (GJSS), Zulaihat Kabir, tare da Auwalu Mai Matasa Pantami, Mahmud Abubakar Wamban Pantami da Hajiya Maimuna Saleh Abdu, sun yi tsokaci kan nasarorin da gwamnatin Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta samu a fannoni daban-daban.

Sun kuma yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu su haɗa hannu da gwamnati wajen tallafa wa mata da yara a faɗin jihar.
Tun da farko, wanda ya assasa shirin, Alhaji Jalo Wali, ya bayyana cewa haɗin gwiwar da suka yi da Alhaji Sa’adu Ali Mai Silifas na da burin raba fakiti ɗari na kayan tsaftar al’ada ga ‘yan mata a makarantun firamare da ke dukkan ƙananan hukumomi goma sha ɗaya na jihar Gombe.

Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kan ‘yan mata kan tsaftar al’ada tare da samar musu da kayan da za su taimaka musu su ci gaba da karatunsu cikin walwala.
Alhaji Jalo Wali ya kuma bayyana Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamna da ya cancanta, tare da yin kira ga al’ummar jihar Gombe su ci gaba da yi wa dukkan ‘yan takarar Jam’iyyar APC addu’ar samun nasara.
A nasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Gombe, Saleh Idris, da Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar wanda Abubakar Muhammad Bello (Bunun Gombe) ya wakilta, sun yaba wa Gombe Charity for Men and Women initiatives Foundation ƙarƙashin jagorancin Alhaji Jalo Wali da Alhaji Sa’adu Ali Mai Silifas bisa wannan shiri na jin ƙai.

Sun yi addu’ar Allah Ya saka musu da alheri tare da ƙara musu ƙarfin gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukan tallafawa mata da ‘ya’yan mata a jihar Gombe.


