Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa
Published: April 19, 2026 at 1:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Raya Kogin Benue ta sanar da wani shiri na musamman domin inganta ayyukan noma ga manoma a yankin Dam ɗin Daɗinkowa da ke jihar Gombe a Najeriya

Manajan Daraktan Hukumar, Dr. Mahmud Sanusi Muhammad, ne ya bayyana wannan shiri ne a yayin ƙaddamar da rabon takin zamani mai rangwame, wanda aka tsara domin ƙara yawan amfanin gona a jihar Gombe.

Domin rage barazanar namun daji, musamman giwayen ruwa Dr. Muhammad ya ce hukumar na duba yiwuwar samar musu da abinci a wurare masu nisa da gonakin mutane. Ya ce wannan zai taimaka wajen jawo su daga yankunan noma, tare da kare rayuwar manoma da amfanin gonakinsu.

Bugu da ƙari, Manajan Daraktan ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin gyaran hanyoyin ruwa (canals), domin kai ruwa zuwa gonaki masu nisa, wanda hakan zai taimaka wajen bunƙasa noman ban-ruwa a duk tsawon shekara.

Sabon Manajan Yanki, Abubakar Muhammad Bello Sarkin Shanu, ya jaddada cewa shirin takin zamani mai rangwame wanda haɗin gwiwa ne tsakanin hukumar da kamfanoni masu zaman kansu na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da wadatar abinci a ƙasa.

Ya ce: “A tsarin da ake ciki yanzu, manoma za su biya rabin kuɗin taki kafin karɓa, sannan su biya ragowar bayan girbi ko dai da kuɗi ko da amfanin gona.”

Sarkin Shanu ya ƙara da cewa irin wannan haɗin gwiwa na da muhimmanci, yana mai jaddada cewa dole ne jama’a su daina dogaro da gwamnati kaɗai.

“Dole mu koya yin haɗin gwiwa domin gina abubuwa masu amfani. Idan aka yi la’akari da yadda yawan jama’a da buƙatu ke ƙaruwa, gwamnati kaɗai ba za ta iya biyan dukkan buƙatunmu ba,” in ji shi.

Wakilan kamfanonin haɗin gwiwa, Yero Farms da Wababe Integrated Agric Ventures, wanda Alhaji Nasiru Umar ya wakilta, sun yaba da ƙoƙarin UBRBDA wajen tallafawa manoma. Sun kuma roƙi waɗanda suka amfana da shirin da su kiyaye amana ta hanyar biyan bashin da aka ba su a kan lokaci.

Taron ya kuma samu saƙonnin fatan alheri daga shugabannin al’umma daban-daban, ciki har da Comrade Musa Umar na Dandalin Matasan Hina da kuma Alhaji Sadik Shehu, Shugaban Ƙungiyar Masu Amfani da Ruwa (WUA).

Duk da yabon shirin, sun roƙi a ƙara faɗaɗa hanyoyin ban-ruwa tare da inganta abubuwan more rayuwa, musamman samar da ruwan sha mai tsafta da wutar lantarki mai ɗorewa a yankin Daɗinkowa da maƙwabtanta.

Da take jawabi a madadin waɗanda suka amfana, Mrs. Doris Yakubu, shugabar mata ta WUA, ta bayyana muhimmancin haɗa mata cikin harkokin noma a yankin.

Ta ce mata a Daɗinkowa na taka rawa sosai a fannin noma, kuma ta nuna kwarin gwiwa cewa tallafin takin zamani zai ƙara yawan amfanin gonakinsu.

Ta kuma tabbatar da cewa manoma za su cika alkawarin biyan bashin da aka ba su bayan samun girbi mai kyau.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Najeriya, Sana'o'i

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma
Next Post: Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC

Karin Labarai Masu Alaka

Zargin Tauye Ka’idojin Zabe: Malam Pantami Ya Janye Daga Takara Afrika
Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista Afrika
Ƙungiyar Mata Sunyi Kira Ga Jam’iyar P R P Da Ta Dauki Baheejja A Matsayin Mataimakiyar Gwamnan A Bauchi 2027 Labarai
Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
  • Iran Da Amurka Sun Gindayawa Juna Ka’idojin Tsagaita Wuta Afrika
  • Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci Labarai
  • Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.