Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci
Published: June 6, 2026 at 4:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya taya Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dr. Abubakar Shehu Abubakar III, murnar cika shekaru 12 da hawansa karagar mulkin kakanninsa.

A cikin sakon taya murnar da ya aike, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana Sarkin Gombe a matsayin amintaccen abokin hulɗa wajen gudanar da mulki, tabbatar da zaman lafiya da kuma bunkasa ci gaba, yana mai yabawa irin kyawawan halayen shugabanci da ya nuna tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2014.

Gwamnan ya ce Mai Martaba Sarkin Gombe ya yi fice wajen jagoranci mai hangen nesa, hikima da sadaukarwa ga ci gaban al’ummarsa, lamarin da ya taimaka matuka wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban tattalin arziki a Jihar Gombe.

Ya kuma yaba wa Sarkin bisa rawar da yake takawa na uba ga al’umma, ayyukan alheri da kuma ƙoƙarinsa na kare da bunƙasa al’adun gargajiyar masarautar Gombe tare da ƙarfafa zaman tare cikin lumana tsakanin al’ummomi mabambanta da ke cikin masarautarsa da ma jihar baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma jinjina wa Mai Martaban bisa jajircewarsa wajen tallafa wa harkokin ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma, musamman shirye-shiryen da ke taimakawa yara marasa galihu wajen samun ingantaccen ilimi.

Har ila yau, ya yabawa Sarkin bisa jagorancinsa a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya da Hakimai ta Jihar Gombe, inda ya ce hakan ya taimaka wajen ƙarfafa rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.

Yayin da yake taya Sarkin murnar wannan gagarumin ci gaba, Gwamna Inuwa Yahaya ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da tsawon rai domin ci gaba da yi wa al’ummarsa hidima cikin nasara da albarka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye

Post navigation

Previous Post: JEI Da Abokan Hulɗar Sun Gudanar Da Aikin Shuka Itatuwa Domin Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya
Next Post: Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
Fadar Shugaban Kasa Ta Karyata Jita-Jitar Yunkurin Sanya Wa Tinubu Guba A Abinci Afrika
Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana Afrika
Tinubu Ya Aika Manyan Hafsoshin Tsaro Borno Afrika
Najeriya Da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Matsalar ‘Yan Gudun Hijira A Najeriya Najeriya
  • Amurka Da Iran Sun Tattauna A Kasar Pakistan Afrika
  • Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye Labarai
  • Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • Sama da mutane dubu 500 ne yanbindiga suka kora daga gidajensu a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
  • Tsohuwar Ministan Albarkatun Mai Ta Bayyana A Kotu Najeriya
  • Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.