Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta
Published: April 23, 2026 at 7:43 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

​Rundunar sojin hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke lura da shiyya ta biyu a Najeriya ta yi nasarar fatattakar wani gagarumin hari da ’yan ta’adda suka kai yankin Kukareta a daren Laraba wayewar Alhamis.

​Harin, wanda aka fara shi jim kadan bayan tsakar dare zuwa misalin karfe 3:00 na asuba, ya gamu da tirjiya daga dakarun soji wadanda suka yi martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa bayan sun tafka asara mai yawa.
​
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar a ranar 23 ga watan Afrilu, 2026, ya bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 24 a yayin artabun.

​Haka kuma, binciken da sojoji suka gudanar a fagen daga bayan kura ta lafa ya kai ga gano dimbin makaman da ’yan ta’addan suka bari, wadanda suka hada da ​Bindigogi kirar AK-47 guda 18 da wasu manyan bindigogi na GPMG guda 3, ​Bindigogin kakkabo jiragen sama (PKT) guda 2 da bututun harba bama-bamai na RPG guda 3 da na Mortar guda 2, ​Guruneti (Hand grenades) guda 4 da kuma dimbin alburusai.

Sanarwar ta kara da cewa sojoji biyu ne suka samu raunuka a lokacin musayar wuta, kuma tuni aka duba lafiyarsu inda suke cikin yanayi mai kyau. Kazalika, wata motar yaki ta sojoji (Tank) guda daya ta samu matsala bayan tayoyinta sun fashe a lokacin da take kai dauki.

A halin yanzu, sojoji na ci gaba da bin sawun ’yan ta’addan da suka tsere da raunuka, inda aka ga alamun jini da kayayyakin magunguna a hanyoyin da suka bi yayin gudun ceton rai.

​Wannan nasara dai ta kara tabbatar da irin shirin da dakarun soji suke da shi na murkushe duk wani yunkuri na ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, inda rundunar ta lashi takobin ci gaba da matsa lamba har sai ta kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin baki daya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya
Next Post: Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna Afrika
Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
Kasashen Daular Larabawa Tare Da Saudiya Da Jordan Sunyi Allah Wadai Da kasar Israel Afrika
Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
Majalisar Dottawa Ta Kafa Komitin Dokar Zabe Najeriya
Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Koriya Ta Arewa Ta Gudanar Da Gwajin Makami Mai Linzami Tsaro
  • NUJ: Akwai Bukatar Samar Da Inshorar Lafiya Ga ‘Yan Jarida A Najeriya Rediyo
  • Sallah Sai Ranar Juma’a A Najeriya: Fadar Sarkin Musulmi Afrika
  • Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki Labarai
  • Samar Da Albarkatun Mai Ya Ragu A Iraq Afrika
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.