Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya
Published: April 22, 2026 at 8:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Aikin Hajjin 2026: Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya

​Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Najeriya (NAHCON) ta kammala shirin tura tawagar jami’anta na musamman zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 27 ga watan Afrilu, domin yin kwasan-kwasai da kuma samar da dukkan abubuwan da suka kamata kafin fara jigilar maniyyata.

​Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin ranar 3 ga watan Mayu, wadda ita ce ranar da aka tsara za a fara jigilar rukunin farko na maniyyatan Najeriya na shekarar 2026 zuwa Saudiyya.

Tawagar, wadda aka fi sani da ‘Advance Team’, ta ƙunshi jami’ai daga sassa daban-daban da suka haɗa da ​Ma’aikatan kula da masaukan alhazzai, ​Jami’an lafiya da masu kula da abinci, ​Tawagar kula da fasfo da kuma jigilar kaya.

​Babban aikin wannan tawaga shi ne tabbatar da cewa an kammala gyara masaukai, an tantance wuraren abinci, kuma an daidaita dukkan tsare-tsaren sufuri domin kauce wa duk wata matsala da za ta iya tasowa lokacin da alhazzai suka fara isa.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa tura jami’an da wuri wani ɓangare ne na sabon tsarin da aka fito da shi domin tabbatar da cewa aikin Hajjin bana ya gudana cikin nasara da natsuwa. Ana sa ran tawagar za ta haɗa gwiwa da hukumomin Saudiyya don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai da tsarin da aka tsara.

​Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da maniyyata a faɗin ƙasar nan suke ci gaba da karɓar bita da kuma shirye-shiryen ƙarshe kafin fara kira na jigilar su zuwa ƙasa mai tsarki.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya
Next Post: Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta

Karin Labarai Masu Alaka

Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Athletic Club Ta Doke Atlético Madrid 3-0, Julian Alvarez Ya Koma Wasa Wasanni
  • Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe Afrika
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
  • Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • UNICEF Ta Tallafawa Jihar Bauchi Da Babura Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.