Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro
Published: April 15, 2026 at 3:21 AM | By: Nasiru Adamu Elhikaya | Updated: April 15, 2026

ADC Ta Kaucewa Matakin INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Da Ya Tabbatar Da Jagorancin David Mark

Jam’iyyar adawa ta ADC ta gudanar da babban taro na kasa ta hanyar kin amincewa da matakin hukumar zabe na gargadin kar ta yi hakan.

Taron dai ya tabbatar da jagorancin Sanata David Mark wanda hukumar zabe ta cire sunansa da mai hamayya da shi a matsayin shugabanni bisa fassarar hukuncin kotu.

“A lokacin da APC ta hau mulki Najeriya na mataki na 8 na a ta’ddanci a duniya. Idan su ka kara wasu shekarun 4 Najeriya za ta dawo ta daya” Inji daya daga manyan ‘yan adawan na ADC Peter Obi wanda ke lissafa yadda gwamnatin Tinubu ta samu kasa da kuma yanda lamura su ke a yanzu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya yi dirar mikiya ne kan shugaban hukumar zabe Joash Amupitan da nuna ba zai sha su a masilla ba da matakan da ya ke dauka na takura adawa.

Adamu Hassan Bunun Kashere na daga mahalarta taron daga Arewa maso gabar, ya ce ba ya raba daya biyu ga tasirin da ADC za ta yi a babban zaben 2027.

Shi ma mukarrabin Peter Obi, Malam Ibrahim Hussaini Abdulkarim na kore tunanin za a samu Baraka a jam’iyyar wajen zaben fidda gwani a tsakanin manyan yan takara da su ka yi dafifi a jam’iyyar.

Taron dai ya gudana da amfani da na’urorin samar da wuta na janareta don tsinke wuta da mai dandalin taron ya yi bisa zargin an umurce shi ne ya yi hakan ko a soke lasisinsa na hurumin gudanar da fagen taruka wato EVENT CENTER na RAINBOW da ke anguwar Garki.

Kazalika taron ya kori shugaban bangare na jam’iyyar Nafiu Bala da wasu ‘yan jam’iyya da jagorancin Mark ya zarga da cin amana.

  1. https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/04/ADC-DEFIES-INEC-HELD-NATIONAL-CONVENTION.mp3
Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara
Next Post: Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala

Karin Labarai Masu Alaka

Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
Kasar Aljeriya Ta Soke Yarjejeniyar Jirgin Sama Tsakaninta Da Daular Larabawa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025 Labarai
  • Magajin Garin Istanbul Dake Kurkuku Ya Bukaci A Gudanar Da Zabe Labarai
  • Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala Afrika
  • Hamma Saleh Ya Yi Fatali da Bai Wa Pantami Takarar Gwamna a PDP Afrika
  • Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe Afrika
  • Amurka Na Shirin Kauracewa Taron Kungiyar Kasashen G20 Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.