Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta a Najeriya wato INEC, ta raba kayan zaɓe masu muhimmanci da za a yi amfani da su a zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilan Tarayya ta Gombe-Kwami-Funakaye.

An raba kayan zaɓen zuwa ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
An gudanar da rabon kayan ne a harabar ofishin Babban Bankin Najeriya, CBN, da ke birnin Gombe.
Jami’in Zaben INEC na Jihar Gombe, Umar Mukhtar Gajiram, ne ya sanya hannu kan kayan zaɓen kafin a raba su, inda ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da aikin.
Gajiram ya bayyana cewa duk wata takardar zaɓe da ba ta ɗauke da sa hannun jami’in da aka tanada ba za a ɗauke ta a matsayin mara inganci.
Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 903 da ke cikin mazabu 31 a ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye.
Jami’in Zaben ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a da su kasance cikin lumana tare da guje wa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan kammala zaɓen.
Haka kuma, ya yi kira ga jami’an zaɓe da su tabbatar da bin ƙa’idoji da ɗabi’un da hukumar INEC ta tanada domin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.
An sanya hannu kan kayan zaɓen ne a gaban jami’an tsaro, jami’an INEC, wakilan jam’iyyun siyasa da kuma wakilan ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye.
Zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilan Tarayya ta Gombe-Kwami-Funakaye dai zai gudana ne ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.


