A wani ɓangare na ayyukan bikin Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta 2026 kungiyoyin fararen hula, shugabannin al’umma da masu sa-kai sun haɗa ƙarfi wajen gudanar da aikin tsaftace muhalli a wasu sassan birnin Kadunan Najeriya tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kare muhalli.
An gudanar da bikin Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya ta 2026 ne ƙarƙashin taken “Daga Faranti Masu Tsabta zuwa Birane Masu Tsabta”, wanda ke jaddada buƙatar rage ɓarnar abinci da kuma inganta tsafta domin samar da al’ummomi masu lafiya da ɗorewar muhalli.
Da take magana yayin aikin tsaftace muhalli a Kaduna, Habiba Suleman, wadda ta shirya ayyukan Ranar Tsaftace Muhalli ta Duniya na 2026 a Kaduna kuma shugabar Plogging Nigeria, Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ce ƙungiyoyi da dama sun shiga aikin da nufin tsaftace wasu sassan Kaduna tare da ƙarfafa wa mazauna garin gwiwa su ƙara ɗaukar nauyin kula da muhallinsu.
Ta ce halartar ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin al’umma da masu sa-kai na nuna muhimmancin haɗin gwiwa wajen magance matsalar gurɓacewar muhalli da kuma sauran ƙalubalen muhalli da ke addabar al’umma.
A cewarta, aikin ba wai tattara shara kaɗai ake nufi da shi ba, har ma da wayar da kan jama’a game da yadda ya kamata a zubar da shara, muhimmancin sake amfani da kayan da za a iya sarrafawa, da kuma buƙatar kiyaye tsaftar wuraren jama’a.
Shi ma da yake magana, Shugaban Sashen Sadarwa da Dabarun Aiki na African Climate Reporters (ACR), Ibrahima Yakubu, ya ce ACR ta shiga aikin tsaftace muhalli ne a matsayin wani ɓangare na ƙudurin ƙungiyar na kare muhalli da kuma yaƙi da sauyin yanayi.
Ya ce kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen ilmantar da jama’a kan yadda ake sarrafa shara, gurɓacewar muhalli da kuma ƙalubalen muhalli da ke da alaƙa da sauyin yanayi.
Ibrahima Yakubu ya jaddada cewa tabbatar da tsaftar Kaduna na buƙatar haɗin kan hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, shugabannin al’umma, ‘yan kasuwa, kafafen yaɗa labarai da kuma mazauna birnin.
Ya ƙara da cewa African Climate Reporters za ta ci gaba da inganta aikin jaridun da suka shafi sauyin yanayi da muhalli, a matsayin wata hanya ta wayar da kan jama’a, ƙarfafa sauyin ɗabi’a da kuma tattara al’umma domin ɗaukar matakan dakile lalacewar muhalli.


