Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Jami’ar ABU Zaria Ta Karbi Kudade Naira Bilyan 1.3 Daga Shirin Nelfund
Published: March 29, 2026 at 2:40 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a jihar Kaduna Najeriya ta tabbatar da karɓar sama da naira biliyan 1.3 daga Asusun Bada Lamunin Karatu (NELFUND) domin tallafa wa ɗalibanta a shekarar 2026.

A wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Maris, 2026, ofishin mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana cewa kuɗin sun kai naira biliyan 1,301,584,250, wanda aka tura cikin asusun jami’ar a matsayin lamunin ilimi ga ɗalibai.

Takardar ta ƙara da cewa kuɗin sun amfanar da ɗalibai 17,599, inda aka raba su kashi uku kamar haka:

• Kashi na farko: ɗalibai 7,570 sun karɓi naira Miliyan 545,144,750

• Kashi na biyu: ɗalibai 7,572 sun karɓi naira Miliyan 571,204,125

• Kashi na uku: ɗalibai 2,457 sun karɓi naira Miliyan 185,235,375

Hukumar jami’ar ta nuna jin daɗinta ga wannan tallafi, tana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa ɗalibai nauyin karatu da kuma inganta harkokin ilimi.

A ƙarshen jami’ar ta gode wa NELFUND bisa rawar da take takawa wajen tallafa wa ɗalibai, tare da jaddada muhimmancin irin wannan shiri wajen bunƙasa ilimi a ƙasar.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja
Next Post: Netanyahu Ya Umarci Rundunar Sojoji Takara Fadada Ayyukanta A Lebanon

Karin Labarai Masu Alaka

An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
Za’ayi Jana’izar Marigayi Ali Khamenei a Tehran, Qom da Mashhad Afrika
Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hamas Ta Mika Ma Isra’ila Gawar Daya Daga Cikin Mutane Biyu Sauran Duniya
  • Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
  • Mamakon Ruwan Sama Da Iska Ya Hallaka Mutane Uku A Jihar Yobe Labarai
  • Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
  • Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
  • Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Bukaci Musulmi Su Rungumi Tausayi Da Ƙaunar Juna Afrika
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.