Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka
Published: January 26, 2026 at 9:27 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yanayin sanyi me tsanani ya lullube sassa da dama na Amurka cikin dusar kankara mai yawa, da ruwan sama me daskarewa zuwa kankara, abinda ya jawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa, har da na jiragen sama.

Bishiyoyi sun fadi tare da tsinkewar layukan wutar lantarki saboda nauyin kankara da ta sauka a kan su, abinda ya haddasa rashin wuta ga dubbannan gidaje da wuraren kasuwanci a kudu maso gabashin kasar.

An yi hasashen cewa kankara tare da dusar Kankara zata ci gaba da saukowa har zuwa ranar Litinin, tare da sanyi me tsanani. Za’a shafe kwanaki cikin yanayin da ka iya kawo hadari ga matafiya kan hanya da ginunnuka, a cewar hukumar kula da yanayi ta kasa.

Dusar kankara me yawa na fadowa daga kwarin Ohio zuwa arewa maso gabashin kasar, yayin da taruwar daskararriyar kankara mai hadari ke barazana ga yankin can kasan kwarin Mississippi, zuwa yankin tsakiyar tekun Atlantika, da kudu maso gabashin kasar.

Da ta ke amsa tambayoyin Manema labarai ta waya, mai hasashen yanayi Allison Santorelli, ta ce wannan yanayi na da ban ne, domin ya ratsa kusan ko ina a kasar, ya Shafi wurare tun daga jihohin New Mexico da Texas, har can zuwa yankin New England. Ta ce abin ya bazu kusan mil 2000 ke nan.

Tun ran Asabar ne, shugaba Donald Trump ya yarda da Sanya dokar ta baci a jihohi kusan 12. Hukumar gudanar da agajin gaggawa ta tarayya ta saka masu bada agaji da kayan aiki a jihohi da dama, a cewar sakatariyar tsaron cikin gida Kristi Noem.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine
Next Post: Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC

Karin Labarai Masu Alaka

Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar Amurka
Dubban ‘Yan Gudun Hijira Sun Halaka Amurka
Sojojin Amurka Sunfara Isowa Gabas Ta Tsakiya Amurka
Kasashen Faransa Da Italiya Sun Nuna Rashin Amincewa Da Matakan Sojoji Amurka
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika
Kungiyar Tsaro Ta NATO Tana Fuskantar Kalubale Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon Wasanni
  • Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya Afrika
  • NSCIA Ta Gargadi Gwamnati Kan Zargin Tauye Haƙƙin Musulmi Afrika
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutane 70 A Nairobi Afrika
  • An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
  • Jirgin Dakon Iskar Gas Daga Rasha Ya Sake Hanya Afrika
  • Najib Razak Zai Kara Shekaru 15 A Gidan Yari Saboda Cin Zarafin Kujerar Mulki Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.