Rahoton Ashiru Alhaji Mukhtari daga Agedez Jamhuriyar Nijar
Hukumomin jihar Agadez da ke jamhuriyar Nijar sun halarci jana’izar mutane 12 da suka rasa rayukansu a ranar Talata, sakamakon wani harin yan ta’adda dauke da manyan makamai suka kai wa motocin fasinja biyu. Lamarin ya auku ne a kimanin kilomita 35 kafin isa birnin Agadez, bayan da motocin suka taso daga garin Arlit.
Daga cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiya har da fasinjoji guda 10 da kuma jami’an tsaro guda biyu wadanda ke kan aikin rakiya. Haka zalika, mutane da dama sun sami raunuka daban-daban a yayin wannan kazamin hari na ba-zata.
Bayanai na nuni da cewa maharan, wadanda ya zuwa yanzu ba a gano ko su wane ne ba, sun kai harin ne da nufin yin awon gaba da dimbin ma’adanan zinare da ake zargin ana jigilarsu a daya daga cikin motocin bas din na kamfanin Sonitrav.
Bayan kammala jana’izar, hukumomin jihar ta Agadez sun jajanta wa iyalai da dangin wadanda lamarin ya shafa, tare da yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.


