Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar
Published: December 24, 2025 at 10:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikata a kasar Masar sun fara harhada wani tsohon jirgin ruwan kwale-kwale na wani fir’auna da ya mulki daular dubban shekaru da suka shige.

Ma’aikata sun fara harhada wannan kwale-kwale a bainar jama’a a sabon makeken dakin kayan tarihi na Masar ranar talata da safe, yayin da ‘yan yawon bude ido suka tsaya su na kallo.

Wannan kwale-kwale mai tsayin mita 42, na wani fir’auna ne, ko sarki, na masar mai suna Khufu, kuma shugaban sashen gyarawa da farfado da kayan tarihi Issa Zeidan yace zasu dauki shekaru hudu suna wannan aiki na sake hada wannan kwale-kwale baki dayansa, yace jirgin ya kunshi katako dai-dai har guda 1650.

Sarki Khufu ya mulki Daular Masar shekatu 4500 da suka shige, kuma shine ya gina babbar dalar nan ta Giza.

Minsitan yawon shakatawa da kula da kayayyakin tarihi na Masar, Sherif fathy, yace wannan aiki yana daya daga cikin ayyukan sake farfado da wani abu na tarihi mafi muhimmanci a wannan karni.

A watan da ya shige aka bude wannan gagarumin dakin ajiye kayayyakin tarihi na Masar wanda aka gina a kan kudi dala maitan dubu 1, inda kuma ake kokarin sake harhada wannan kwale-kwale, kuma aikin tarihin yana dauke da kayayyaki kusan dubu 50, cikinsu har da kayayyakin da aka samo daga cikin kabarin sanannen Fir’aunan nan mai suna Tutankhamun wanda aka gano a shekarar 1922.

Wannan kwale kwale da ake kokarin sake harhadawa yana daga cikin wasu guda biyu da aka gani a shekarar 1954 a gefen bangaren kudu na Dalar Giza, an fara tono shi daga inda yashi ya binne shi a shekarar 2014.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Amurka Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashe Hudu Domin Inganta Kiwon Lafiya
Next Post: Kotu A Birnin Tarayya Abuja Ta Bada Belin Tsohon Minista Abubakar Malami

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya Afrika
Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika
Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika
China Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Kulla Yarjejeniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu: Ku Guji Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi Najeriya
  • Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
  • Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika
  • Akwai Doka Mai Tsanani Wajen Mallakar Bindiga A Kasashen Yammacin Turai Labarai
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jadda Da Aniyar Rage Radadin Talauci Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.