Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji
Published: December 7, 2025 at 3:30 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 7, 2025

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Benin da sojoji domin daƙile juyin mulkin da wasu sojoji suka yi iƙirarin yi.

Matakin na Ecowas na zuwa ne bayan wani rukunin soji sun sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a ranar Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin “duk wani rai da aka rasa” sakamakon yunƙurin nasu.

“Ecowas za ta taimaka wa gwamnati da al’umma da duk abin da ya kamata, ciki har da aika dakarun ko ta kwana domin kare tsarin mulki da kuma ‘yancin Benin,” a cewar sanarwar da hukumar Ecowas mai hedikwata a Abuja ta fitar

Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.

“An shawo kan lamarin sannan mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban ƙasa baya haja kuma muna ƙara shawo kan al’amuran.” kamar yadda Ministan harkokin waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

Afrika

Post navigation

Previous Post: An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin
Next Post: ‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Malaman Makaranta A Tilabery

Karin Labarai Masu Alaka

Makiyaya Sun Shiga Matsala Sakamakon Fari A Kasar Kenya Afrika
Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil Afrika
Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
NUT Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
  • Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Hari Da Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Mutane Da Dama A Darfur Labarai
  • Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya Labarai
  • Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
  • Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya Afrika
  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.