Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Netanyahu Yayi Gaggawar Amincewa Da Kasafin Kudin Kasar
Published: March 26, 2026 at 6:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na gaggauta kokarin amincewa da kasafin kudin ƙasa domin kauce wa zabukan wuri-wuri da ake ganin zai iya sha kaye a cikinsu, yayin da yakin da ake yi da Iran bai kawo wani gagarumin sauyi a yadda ake kallonsa a kuri’un jin ra’ayin jama’a ba.

A kwanakin farko na yakin, bangaren Netanyahu ya ga wata dama ga kawancen jam’iyyunsa na dama su amfana da harin farko da ya kashe Ayatollah Ali Khamenei, ta hanyar gudanar da zabuka kafin lokacin da ake sa ran yi a watan Oktoba, kamar yadda wata majiya mai masaniya kan dabarun siyasarsa ta bayyana.

Daya daga cikin hanyoyin tilasta gudanar da zabukan gaggawa ita ce a bar majalisar dokoki ta kasa amincewa da kasafin kudin kafin ranar 31 ga Maris, wanda a karkashin dokar Isra’ila zai jawo gudanar da zabe cikin kwanaki 90. Yayin da hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila suka kashe manyan jami’an Iran da dama, wasu na kusa da Netanyahu sun fito fili suna hasashen yiwuwar gudanar da zabe a watan Yuni.

Sai dai kusan makonni hudu da fara yakin, wanda har yanzu bai cimma daya daga cikin manyan manufofinsa na kifar da gwamnatin malaman addini ta Iran ba, firaministan Isra’ila mafi dadewa a mulki na kokarin kauce wa zabukan wuri-wuri, kamar yadda mambobi uku na gwamnatinsa suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Afrika, Labarai, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji A Jihar Kebbi
Next Post: Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai

Karin Labarai Masu Alaka

NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i Afrika
Dakarun Sakai A Kasar Sudan Sun Kashe Mutane 28 A Wani Farmaki Afrika
Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
An Zargi Babban Mai Gabatar Da Kara A Kotun Duniya Ta ICC Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
  • Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya Afrika
  • An Kashe Mutane 169 A Wani Harin Sudan Ta Kudu Afrika
  • Babu Dabbar Da Zata Sake Shiga Amurka Daga Mexico! Amurka
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.