Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da kamfanin sarrafa ma’adinin Lithium mafi girma a jihar Nasarawa.
Bikin kaddamar da masana’antar da kamfanin makamashi na Diamond New Energy ya gina, ya gudana ne a ranar Alhamis, a yankin Endo a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

Shugaba Tinubu yace kaddamar da ayyukan samar da makamashi ya nuna karbuwar Najeriya, a idon duniya da kuma sauye-sauye masu inganci da gwamnati mai ci take yi.
Tinubu ya kara da cewa Najeriya a shirye ta ke ta shiga cikin tattalin arzikin ma’adinai na duniya bisa sharuddan samar da ayyukan yi, gina kwarewa, karfafa masana’antu na cikin gida, da fadada ginshiki mai albarka.

Shugaba Tinubu ya ce Lithium ya zama daya daga cikin ma’adanai dake samadda canji na makamashi a fasahar sarrafa baturi, lantarki da sauransu.
Shugaban wanda mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari mai yawa a fannin sarrafa lithium da makamashi domin habaka tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma samar da ababen more rayuwa a Najeriya.
Ya jaddada cewa ma’adanai masu ƙarfi sune kashin bayan kowace tattalin arziki, domin babu wata fasaha da ke tasowa ba tare da su ba.
Tinubu ya ci gaba da cewa, a duk fadin duniya, kasashen da suke albarkatun ma’adanai, man fetur, iskar gas, filaye masu albarka, da kuma wurare masu kyawun yanayi, sun kasance cikin tarnakin talauci saboda sun kasa mayar da wadannan albarkatun zuwa ababen da zasu amfanesu.

Ya ambaci kasashen Japan, Singapore, Koriya ta Kudu, har ma da China, kan yadda suke taka rawa wajen wadata al’mmarsu da fasaha da suke dashi da samarda ayyukan yi daga albarkatun kasa.
“Saboda haka, ina tare da ku a yau a madadin shugabana, mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, kuma tare da yardarsa a gare ku, mun taru don tabbatar da wata alkibla, don yin bayani game da irin yadda tattalin arzikin Nijeriya ya kamata ya zama, irin makomar da ya kamata mu gina, da kuma irin haɗin gwiwar da ya kamata mu karfafa idan abubuwan da muke da su na ma’adinai za su juya zuwa ga ci gaban al’umma.
Da yake jawabi, gwamna jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce, baya ga albarkar kasa domin noma jihar tana kuma da albarkatun kasa daban-daban da suka hada da, Lithium, Barrett, Kwal, Marvuls da sauransu.
Daga nan sai gwamnan ya yabawa gwamnatin tarayya da ma’aikatar ma’adanai ta kasa bisa goyon bayan jihar don samun nasarar gyara kamfanin sarrafa Lithium mafi girma a Afirka ta Yamma domin ganin Nasarawa ta kasance daya daga cikin jihohi masu inganci a kasar.
A nasa jawabin, ministan albarkatun ma’adinai, Mista Dele Alake, ya ce jihar Nasarawa tana da albarkatun kasa da a baya aka yi watsi da su, wanda kuma ke ba da damammaki a ci gaban tattalin arziki musamman a arewacin kasar baki daya.
Ya ce saboda masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ma’aikatarsa ta dauki nauyin rundunar ta musamman domin kare ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba inda aka kama sama da mutane 300, wasu kuma na fuskantar shari’a.


