Injiniya Dr. Usman Maijama’a Kallamu ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Gombe, Kwami da Funakaye.
An gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Zaɓen, Dr. Habu Dahiru, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Gombe, tare da halartar jami’an hukumomin zaɓe da suka sanya ido kan yadda aka gudanar da aikin.
Da yake gabatar da tsarin zaɓen, Dr. Habu Dahiru ya bayyana ƙa’idoji da matakan da za a bi wajen gudanar da zaɓen, kafin ya gabatar da wakilan jam’iyyar da aka tantance daga ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye waɗanda suka cancanci kaɗa kuri’a.
Daga nan ne aka ayyana Injiniya Dr. Usman Maijama’a Kallamu a matsayin wanda ya yi nasara ba tare da hamayya ba, bayan dukkan wakilan jam’iyyar APC da aka tantance daga ƙananan hukumomin uku sun amince da shi baki ɗaya.
A jawabinsa na karɓar takarar, Injiniya Dr. Usman Maijama’a Kallamu ya nuna godiya ga al’ummar mazabar bisa amincewar da suka nuna masa da kuma zaɓar sa domin ya wakilce su ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.
Ya yi kira ga sauran masu neman takarar da magoya bayansu da su haɗa kai tare da yin aiki tare domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a dukkan matakai.
Tun da farko, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwami, Alhaji Ibrahim Buba Makama, ya yaba wa Kwamitin Zaɓen ƙarƙashin jagorancin Dr. Habu Dahiru bisa yadda ya gudanar da zaɓen fidda gwani cikin nasara.
Ya kuma yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki a mazabar bisa haɗin kai da jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara.


