Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed
Published: July 1, 2026 at 3:15 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: July 1, 2026

Tawaga daga Gwamnatin Jihar Benue, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, tare da tawagar Ƙungiyar Makiyaya ta Najeriya (MACBAN) wadda Sakataren ƙungiyar na Kasa ya jagoranta, sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Ardo Risku Mohammed, tsohon Shugaban MACBAN na Jihar Benue.

Tawagogin sun kai ziyarar ne domin jajanta wa iyalan marigayin, ‘yan uwansa da al’ummar yankinsa bisa rasuwarsa mai ban tausayi. Sun kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa, ‘ya’yan ƙungiyar MACBAN da daukacin al’umma haƙurin jure wannan babban rashi.

A yayin ziyarar, tawagogin sun jaddada muhimmancin tabbatar da adalci, zaman lafiya da haɗin kan al’umma. Sun buƙaci iyalan marigayin da su kasance masu haƙuri da juriya, tare da tabbatar musu cewa za a ci gaba da ƙoƙarin ganin an tabbatar da adalci da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Haka kuma, tawagogin sun bayyana cewa rasuwar marigayi Alhaji Ardo Risku Mohammed babban rashi ne ga iyalansa, ƙungiyar MACBAN da ma al’ummar Jihar Benue baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Uncategorized

Post navigation

Previous Post: An Tsaurara Tsaro Yayin Da Tehran Ke Shirin Karɓar Masu Jimamin Ayatollah Khamenei
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa

Karin Labarai Masu Alaka

Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika
Al’ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta sharewa gidaje sun Koka. Najeriya
Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a Amurka
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Harin Da Israela Ta Kai Gaza Yayi Ajalin Mutane 27 Da Yara Uku Labarai
  • Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
  • Tabbas Za’a Gudanar Da Gasar Firimiya Lig Ta Najeriya Wasanni
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
  • Mourinho Ya ƙara Ta’azzara Takaddamarsa Da Hukumomin ƙwallon ƙafar Turkiyya Wasanni
  • Amy Hunt Ta Zama Sabuwar Tauraruwar Wasannin Guje-guje Ta Birtaniya Wasanni
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.