Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Kasar China Ta Daina Bada Bashi Da Dalar Amurka Sai Da Kudin Kasar Yuan
Published: January 22, 2026 at 8:43 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A karon farko tun bayan bullar annobar cutar COVID-19, yawan basussukan da kasar China ta bawa kasashen Afirka a shekarar 2024 ya ragu da fiye da rabi zuwa dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 100.

Wasu alkaluma da Jami’ar Boston a Amurka ta fitar ranar laraba sun nuna cewa wannan adadin, wanda bai kai ko kashi 10 cikin 100 na rancen dala Biliyan 28 da miliyan 800 da China ta ba kasashen Afirka a shekarar 2016 ba, sun nuna yadda kasar take kaucewa daga manyan ayyuka kamar gina layukan dogo na jiragen kasa da hanyoyin mota, zuwa ga kananan ayyukan da za a iya samun riba daga gare su.

China ta fuskanci hasarar wasu daga cikin kudaden da ta bayar bashi a bayan da koma-bayan tattalin arzikin da ta biyo bayan annobar COVID-19 ta jefa kasashen Zambiya, Ghana da kuma Ethiopia cikin yanayi na kasa biyan basussukan da suka karba.

Haka kuma, binciken jami’ar ya nuna cewa a yanzu China ta daina bayar da basussuka na Dalar Amurka, ta koma ga wadanda ake bayar da su da takardar kudin Yuan na kasarta.

Binciken ya nuna cewa a shekarar 2024 ga misai, duk basussukan da China ta ba kasar Kenya an lissafa su ne da takardar kudin Yuan. Haka kuma a cikin watan Otoba, Kenya ta sauya basussukan dalar Amurka biliyan 3 da rabio da China ke binta, ta maida su suka koma na takardar kudin Yuan.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Tarayya: Bikin Al’adun Argungu Ya Karbu A Idon Duniya
Next Post: Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
Sabon Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khameni Yaji Rauni Kuma Ya Nakasa Afrika
Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Babu Musguna Wa ’Yan Jarida A Mulkin Tinubu Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Gana Da Shugaba Tinubu Siyasa
  • Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
  • Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai Najeriya
  • Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
  • Za’a Bude Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Ta Duniya 2026 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.