Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gombe Ta Ƙarfafa Matasa da Ƙwarewar da Za Ta Kai Su Masana’antar Mai Da Iskar Gas
Published: June 22, 2026 at 3:48 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe, tare da haɗin gwiwar Kamfanin Rift Oil Petroleum Company Limited da ke Abuja, ta ƙaddamar da wani shirin horaswa na musamman ga matasa da masu sana’o’i sama da 100 daga ƙananan hukumomi 11 na jihar, domin inganta ƙwarewarsu da shirya su don cin gajiyar damar aiki a fannin mai da iskar gas.

An fara gudanar da shirin ne a Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da Emerald Hotel da ke Gombe, yayin da jihar ke ci gaba da shirye-shiryen farfaɗo da ayyukan bincike da haƙar mai a yankin Kolmani.

Da yake ƙaddamar da shirin, Babban Sakataren Ma’aikatar Makamashi da Albarkatun Ma’adanai ta jihar, Alhaji Suleiman Musa Kwami, ya bayyana cewa manufar horaswar ita ce samar da ƙwararrun ma’aikata na cikin gida da za su iya taka rawa a ci gaban masana’antar mai da iskar gas da ake sa ran za ta bunƙasa a jihar.

Ya ce ma’aikatar ta karɓi buƙatun shiga shirin sama da 400 daga matasa masu sha’awar cin gajiyar damar da fannin zai samar, yana mai yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa goyon bayan da gwamnatinsa ke bayarwa wajen bunƙasa albarkatun makamashi da haɓaka ƙwarewar matasa.

A nasa jawabin, Daraktan Kimiyya, Fasaha da Ilimin Sana’o’i na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Aminu Shehu, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar na ƙarfafa matasa ta hanyar koyar da sana’o’i da dabarun zamani da za su taimaka musu samun ayyukan yi.

Shi kuwa mai ba da shawara ga Kamfanin Rift Oil Petroleum Company Limited, Mista Samson Mato, ya buƙaci mahalarta shirin da su mayar da hankali wajen cin moriyar horon, yana mai cewa ƙwarewar da za su samu za ta ƙara musu damar samun aiki a masana’antar mai da iskar gas a faɗin ƙasar nan.
Hakazalika, Ahmad Ardo Muhammad ya jaddada muhimmancin shirin wajen samar da ƙwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kamfanin Rift Oil Petroleum Company Limited kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Injiniya Rabiu Suleiman, ya ce an tsara shirin ne domin wayar da kan al’umma game da muhimmancin masana’antar mai da iskar gas a matsayin wata muhimmiyar hanyar samar da kuɗaɗen shiga da haɓaka tattalin arziki.

Ya kuma yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda matakan da take ɗauka na tabbatar da cewa Gombe ta amfana da albarkatun mai da ke yankin Kolmani tare da shiga sahun jihohin da ke samar da mai a Najeriya.

Shirin horaswar zai mayar da hankali ne kan fannoni da suka haɗa da girke-girken lantarki da kula da shi, walda da ƙera kayayyaki, aikin kafinta, aikin famfo da sauran sana’o’in fasaha masu alaƙa da harkar mai da iskar gas.

Afrika, Kimiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki
Next Post: Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
An Ga Watan Ramadan A Najeriya Da Nijar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen Afrika
Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a Labarai
  • Tattalin Arzikin Kasar Botswana Zai Farfado Afrika
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
  • Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
  • Rundunar Operation Endurance Peace Ta Gano Wajen Kera Makamai A Jihar Filato Afrika
  • Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.