Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma
Published: June 21, 2026 at 8:18 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafin Kayan Aikin Noma (FISP) a yankin Arewa maso Yamma, inda aka raba buhunan taki 100,800 ga ƙananan manoma 25,200 a jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi da Jigawa.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a jihar Katsina, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa samar da abinci da kuma haɓaka tattalin arzikin karkara, daidai da manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

Ministan ya bayyana cewa kowace daga cikin jihohin biyar da suka ci gajiyar shirin ta samu buhunan taki 20,160, waɗanda za a raba wa manoma 5,040 da aka yi wa rijista tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN).

A cewarsa, manufar shirin ita ce rage gibin da ke tsakanin ƙananan manoma da manyan manoma ta fuskar yawan amfanin gona, tare da tallafa wa masana’antun taki na cikin gida domin ƙara yawan samar da taki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tsarin samar da abinci a ƙasar nan.

Sanata Kyari ya tunatar da cewa a baya gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin AgGrow-1, wanda ya haɗa masu sarrafa kayan amfanin gona da manoma da aka yi wa rijista domin tabbatar da samun kasuwa ga amfanin gonarsu da kuma inganta darajar noma.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi samar da wadataccen abinci, waɗanda ke taimakawa wajen daidaita farashin kayan abinci, rage matsin hauhawar farashi da kuma ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arzikin noma a Najeriya.

“Ba a samun nasarar samar da wadataccen abinci a rana ɗaya. Ana samun ta ne a kowace kaka, ta hanyar kowane manomi da kuma kowane kayan tallafin noma da aka samar. Yau yankin Arewa maso Yamma ne ya samu wannan dama,” in ji Ministan.

Shirin na FISP na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci a faɗin ƙasar nan.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal
Next Post: An Karrama Darakta Janar Na DSS Bisa Ƙoƙarinsa Na Inganta Alaƙar Hukumomin Tsaro Da Kafafen Yaɗa Labarai

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Amurka Tana Ganawa Da Manyan Jami’an Leken Asiri Amurka
  • An Kashe Sojojin Bangladesh A Kasar Sudan Tsaro
  • Hukumomin Tsaron Najeriya Ne Suka Bukaci Amurka Ta Turo Musu Sojoji Amurka
  • Burkina Faso Ta Sako Jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya 11 Da Aka Tsare Tsaro
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami Tsaro
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.