Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo
Published: January 26, 2026 at 8:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu ‘yan kungiyar ‘yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar ISIS a gabashin Congo sun hallaka a kalla mutane 25 a cewar masu rajin kare hakki a lardin Ituri.

Wadanda aka kashe sakamakon harin da kungiyar Allied Democratic Forces, wato IDF ta kai, sun hada da maza 15 da aka kone da ran su a wani gida, da wasu 7 da aka harbe a kauyen Apakulu, a yankin Irumu da ke lardin Ituri. Uku kuma an kashe su ne a yankin gudanar da ayyuka na Walese Vonkutu.

Shugaban kungiyar masu rajin kare hakki, Christophe Muyanderu, yace abun ya faru wajajen karfe 4 na asuba, inda rayuka a kalla 25 suka salwanta. Ya kara da cewa wannan hari na ADF kisan gilla ne karara.

Ba’a ji daga kungiyar ta ADF kan lamarin ba.

Jamhuriyar Demokradiyar Congo dai na yawan samun hare-hare a watannin baya bayan nan daga kungiyoyin ‘yan tawaye da suka hada da ADF kuma kungiyar M23 da kasar Rwanda ke marawa baya.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki
Next Post: Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
Shugaba Trump Ya Kara Matsin Lamba Kan Iran Amurka
Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika
An Kashe Sojojin Bangladesh A Kasar Sudan Tsaro
Isra’ila Ta Kashe Babban Jami’in Tsaron Iran Ali Larjani Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya Afrika
  • Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa Afrika
  • Gombe Da UNFPA Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Yaƙi Da Cutar Fistula Da Tamowa Afrika
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ruwan Sama Ya Dai-Daita ‘Yan Gudun Hijira A Gaza Labarai
  • Shugaba Trump Ya Janye Karbar Kudin Fito Daga Wasu Kasashen Turai Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.