Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa
Published: April 2, 2026 at 6:48 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Amurka za ta “fice daga Iran cikin gaggawa” kuma za ta iya komawa domin kai “hare-hare lokaci zuwa lokaci” idan akwai bukata, a cewar shugaba Donald Trump, wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba, sa’o’i kaɗan kafin ya gabatar da jawabi ga al’ummar ƙasar a daren laraba game da yaƙin.

Yayin da rikicin ya shiga mako na biyar, kuma Trump ke fuskantar matsin lamba kan yadda zai kawo ƙarshen rikicin, sakamakon hauhawar farashin mai, shugaban ya tsara yin jawabi da ƙarfe 9 na dare domin bayyana matakin da za a ɗauka gaba. Jawabin nasa zai rufe wata rana da ta fara da ziyarar tarihi da Trump ya kai Kotun Koli.

Trump, a wata hira ta wayar tarho da Reuters, ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan jawabin nasa shi ne bayyana rashin jin daɗinsa da ƙungiyar NATO, saboda abin da yake ganin rashin goyon bayan da ƙungiyar ke bayarwa ga manufofin Amurka a Iran.

Rikicin siyasa tsakanin Amurka da ƙawayenta na Turai ya ƙara tsananta, a zangon mulkinsa na biyu bayan da ƙasashen Turai suka ƙi amincewa da bukatarsa na taimakawa wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar man fetur ta mashigar Hormuz.

Ya ce yana “la’akari ƙwarai” da yiwuwar fitar da Amurka daga NATO, wata ƙungiyar yarjejeniya da Majalisar Dattawan Amurka ta amince da ita tun a shekarar 1949. A baya ma Trump ya taɓa nuna sha’awar janyewa daga ƙungiyar, sannan kuma ya samu nasarar matsa wa mambobinta lamba su ƙara kashe kuɗi wajen harkokin tsaro.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Mabiya Dariqar Tijjaniyya Sunfara Gudanar Da Addu’oi Saboda Tsare Sheikh Sani Khalifa Zariya
Next Post: Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wasu Wakilai

Karin Labarai Masu Alaka

Kungiyoyin Fararen Hula A Gombe Sun Bukaci A Bawa Mata Jagoranci Afrika
Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika
Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai
  • Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland Amurka
  • Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Garo A Matsayin Mataimakinsa Na 2027 Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.