Daga Zainab Babaji a Jos
Sashen kula da muhimman kadarori da kare ababen more rayuwa a ofishin mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya nemi hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) don inganta rahotanninsu da dakile labaran karya da karfafa wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi muhimman ababen more rayuwa na kasa.
Tawagar ta yi wannan roko ne a wata ziyarar fahimtar da ta kai Sakatariyar ‘yan jarida ta Najeriya a Abuja, inda tattaunawarsu ta ta’allaka kan rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen kare muhimman ababen more rayuwa, inganta tsaron kasa da kuma tabbatar da cewa jama’a sun samu sahihan bayanai masu inganci.
Tawagar ta bayyana damuwarta kan yadda ake yada labaran karya, musamman rahotannin da suka shafi kafafen sadarwa da sauran masu samar da sabis, inda ta nuna cewa rashin isar da sahihan bayanai na iya zamewa yaða bayanan karya ga jama’a da hakan zai raunana amincewar al’umma da kasarsu.
Daraktan sashen, Air Vice Marshal Effiom, wanda ya jagoranci tawagar, ya bukaci ‘yan jarida da su kiyaye ka’idojin aikinsu ta hanyar gudanar da cikakken bincike da tabbatar da bayanai kafin wallafawa ko watsawa.
Ya kuma yi kira ga kungiyar ta NUJ da ta samar da tsari da zai tabbatar da kafafen yaða labarai suna bada sahihan labarai kan kafafen sadarwa da sauran muhimman masu samar da sabis.
Da yake mayar da martani, Shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa, Kwamared Alhassan Yahya, ya yaba wa tawagar bisa amincewa da kungiyar a matsayin babbar abokiyar huldar abokantaka wajen ciyar da tsaron kasa gaba da kuma moriyar jama’a.
Yahya ya ba tawagar tabbacin aniyar kungiyar na yin hadin gwiwa da hukumar, yana mai jaddada cewa aikin jarida na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa, wayar da kan jama’a da kuma inganta muradun kasa baki daya.
Ya bayyana kudurin kungiyar ta NUJ na tallafawa shirye-shiryen da za su karfafa aikin jarida da kuma sanya ‘yan jarida a matsayin wakilai masu kawo sauyi mai kyau a harkar yada labarai da kasa baki daya.
Shima da yake jawabi, Sakataren NUJ na kasa, Mista Achike Chude, ya jaddada bukatar samar da tsayayyen tsari don jagorantar hadin gwiwar da ake shirin yi.
Ya bayyana mahimmancin tsarin haɗin gwiwa tsakanin Ƙungiyar da Hukumar, da kuma shirye-shirye na ƙarfafawa don ba wa ‘yan jarida ilimi da basirar da ake bukata don bayar da rahoto mai inganci game da muhimman kadarorin kasa, da kuma batutuwan tsaro.
Ziyarar ta ba da dama ga bangarorin biyu su duba hadin gwiwa, da inganta aikin jarida sahihi, cikin da’a, da sanin ya kamata, don tallafawa tsaron kasa da moriyar jama’a.


