Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro Afrika
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN Afrika
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira Afrika
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe Afrika
  • An Horar Da Mata Kan Sarrafa Abinci Mai Gina Jiki A Gombe Afrika

Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84%
Published: October 19, 2025 at 3:09 AM | By: Newsdesk | Updated: November 15, 2025

Mizanin karfin tattalin arzikin Najeriya a rubu’in karshe na shekara ta 2024 ya karu da kashi 3.84% daga kashi  2.74% a 2023.

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta saki rahoton da ya nuna sassan da ke waje da danyen man fetur ne ke kan gaba wajen raya arzikin.

“Masu neman bayani kan mizanin farashi CPI sun sauke rahoton fiye sau dubu 500 a shekara 6 da ta wuce. Don haka wannan rahoto da na mizanin arziki GDP ya zama mai muhimmanci da mu ke fitarwa bisa bin ka’idoji na duniya” Inji shugaban hukumar kididdigar Prince Adeyemi Adeniran.

Alkaluman sun nuna bangaren sufurin jirgin kasa, mota, sadarwa da cibiyoyin kudi na kan gaba wajen karfin hada-hadar arziki a Najeriya.

Babban jami’I na hukumar ta NBS Ibrahim Yakubu Tanko ya yi karin haske da nuna mizanin na GDP ya na duba dukkan hada-hada ce ta kudi kuma a kan sabuta shi bisa tafiyar zamani “akwai sana’o’I da a da ba mu sa su ba kamar harka na yanar gizo. Ga kuma harka ta sufurin yanar gizo kamar UBER da kasuwancin JUMI’A, wadannan hanyoyi sun yi karfi don a wasu kasashen ma su ne hanyoyin kasuwancin”

A nan hukumar ta NBS ta yi karin bayani kan mizanin farashin kaya CPI da wasu kafafen labaru su ka yi kuskuren fahimtar rahoton da ba wai ya na nuna saukowar farashi ba ne daga kashi 34% zuwa 28.4% amma sauya shekarar da a ke gwada lissafin tsada daga 2009 zuwa 2024 ya kawo bambancin bisa ma’anar yanzu a kan gwada ma’aunin ne daga bara inda dama kaya sun yi tsada.

Kwarerre a fannin mizanin farashi Dokta Abdullahi Jibrin ya duba amfanin mizanin tun da ba ya na nuna saukar farashi a kasuwa ba ne “idan gwamnati za ta daidaita albashi ta na amfani da wannan hauhawa ne. Babban banki kan yi amfani da alkaluman wajen karawa ko rage kudin ruwa. Talakawa ma kan yi amfani da ma’aunin wajen sarrafa kudin su”

NBS ta saki rahoton mizanin farashi da na tattalin arziki daidai lokacin da kayan masarufi su ka dan sauka a kasuwa wanda ke da alaka da shigo da abinci daga ketare da kuma kara darajar canjin Naira kan dalar Amurka.

Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya
Next Post: Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993

Karin Labarai Masu Alaka

Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
Hukumar Lafiya A Gombe Ta Bukaci Iyaye Su Tallafa Wa Gangamin Rigakafin Tetanus Kimiya
Najeriya @ 66: Tinubu Ya Ce Gwamnati Za Ta Kara Zuba Jari A Noma, Masana’antu Da Bunƙasa Matasa Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Masana: ‘Yancin Kasashen Afrika A Rubuce Yake Ba A Zahirance Ba Najeriya
CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gombe: ’Yan Sanda Da NSCDC Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
  • Tsadar Gidajen Haya Na Jefa Iyalai Cikin Wahala A Arewacin Najeriya — PRRFN
  • DPO Ya Harbe Almajiri Har Lahira
  • NSCDC Ta Kama Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Wayoyin Lantarki Da Kisan Kai A Gombe
  • Tinubu Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Sake Zaɓensa A 2027

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Ya Karbi Shaidar Jam’iyar APC Siyasa
  • Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
  • Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
  • Kasar Habasha Da Turkiyya Sun Kulla Yarjejeniyar Makamashi Afrika
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.