Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen lalata muhimman kayayyakin more rayuwa da kuma kisan kai, tare da kwato kusan mita dubu guda na wayoyin wutar lantarki da aka lalata a wasu ayyukan sintiri daban-daban a jihar.
Da yake yi wa manema labarai bayani a Gombe, Kwamandan hukumar na jihar, Mohammed Inuwa Usman, ya ce an samu nasarorin ne sakamakon tattara bayanan sirri tun da wuri da kuma haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’ummomin yankunan.
Da yake ƙarin bayani kan batun lalata kayayyakin more rayuwa, kwamandan ya bayyana cewa an kama wani matashi mai shekaru 22, mai suna Abdulrahman Ali, mazaunin Tudun Wadan Pantami, bisa zargin yanke wayoyin wutar lantarki masu sulke da ke samar da wuta ga ma’ajiyar man fetur ta kamfanin NNPCL da ke kan titin Bauchi.
Bisa ga bayanan binciken farko, an ce marigayin ya bugi wanda ake zargin da sanda a lokacin da suke musayar kalamai, lamarin da ya sa Mohammed ya mayar da martani ta hanyar caka masa almakashi, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Hukumar ta ce jami’an NSCDC sun kama wanda ake zargin nan take a wurin da lamarin ya faru.
Kwamanda Usman ya tabbatar wa al’umma cewa hukumar za ta ci gaba da tabbatar da bin doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai cewa binciken da ake gudanarwa kan dukkan lamuran ya kusa kammalawa.
Ya ce: “Hukumar a ƙarƙashin jagorancina za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare muhimman kadarori da kayayyakin more rayuwa na ƙasa, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.”
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargin a gaban kotun da ta dace bayan kammala bincike.


