An jaddada muhimmancin sauye-sauyen dokokin haraji na shekarar 2025, waɗanda suka keɓe mutanen da kuɗin shigarsu bai wuce naira dubu ɗari takwas a shekara ba daga biyan harajin kuɗin shiga na mutum, a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Gombe, domin inganta ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
Mai kula da shiyyar Hukumar Kula da Haraji ta Najeriya (Nigeria Revenue Service), Danjuma Manga, ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa na shekarar 2026 da Ƙungiyar Shugabannin Ma’aikatun Tarayya da Hukumomin Gwamnati ta shirya, mai taken “Daidaita Manufofin Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi Domin Samar da Ci Gaba Mai Ɗorewa a Ƙasa.”
Danjuma Manga, wanda kuma yake kula da ayyukan hukumar a jihohin Adamawa, Gombe da Taraba, ya bayyana cewa mutanen da suke samun mafi ƙarancin albashi na ƙasa, wato naira dubu saba’in a wata ko ƙasa da haka, ba sa biyan harajin kuɗin shiga na mutum.
Ya ce wajibcin biyan haraji yana tasowa ne idan mutum ya samu kuɗin shiga, ya ci riba ko kuma ya samu kuɗi daga sayar da kadarorinsa.
Manga ya ƙara da cewa sabbin sauye-sauyen dokokin haraji sun haɗa da sauye-sauyen rabon kuɗaɗen shiga tsakanin matakan gwamnati, inda Gwamnatin Tarayya ta amince ta rage kaso biyar cikin ɗari daga nata kaso domin bai wa gwamnatocin jihohi.
A nasa jawabin na musamman, Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Tarayya, Farfesa Yusuf Abdullahi, ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa shirye-shiryen ci gaba sun isa ga al’ummomin da suka fi buƙata.
Ya bayyana cewa shirye-shiryen kula da masu fama da cutar kansa, musamman kansar nono, mahaifa da ta prostate, na daga cikin fannoni da ke buƙatar tsare-tsare na bai ɗaya, inda ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙaddamar da shirye-shiryen gwaji domin samar da magani kyauta ga wasu zaɓaɓɓun masu fama da cutar kansa.
Farfesa Abdullahi ya buƙaci hukumomin gwamnati da su kauce wa gudanar da ayyuka ba tare da haɗin kai ba, su rungumi shirye-shirye na bai ɗaya waɗanda za su inganta rayuwar al’umma kai tsaye.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Hukumomin Tarayya a jihar Gombe, Comrade Sadiq Ahmed, ya ce taron ya ƙara fahimtar hukumomin tarayya game da rawar da suke takawa wajen ci gaban jihar.


