Rundunar ’Yan Sandan jihar Bauchi a Najeriya ta kama mutum goma sha bakwai (17) bisa zargin aikata laifukan haɗa baki, ɓata suna, shiga gida ba bisa ƙa’ida ba, tsoratarwa, yunƙurin kisan kai da lalata kadarori, sakamakon wani mummunan hari da ake zargin ya samo asali daga zargin maita a ƙauyen Gobirawa.
Lamarin, wanda ya nuna illar ɗaukar doka a hannu da kuma munanan akidu na camfi, ya faru ne a ranar 18 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe ɗaya na dare, a ƙauyen Gobirawa da ke gundumar Gwana, ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Bisa ga rahoton da aka samu, waɗanda ake zargin sun haɗa baki da wasu mutum uku da suka tsere, waɗanda su ne Maharazu Isah, Babangida Kadamaje da Yakubu Umaru, inda suka kutsa cikin gidan wani mutum mai shekaru 60 da ke wannan ƙauye, ɗauke da adduna da sanduna.
A yayin harin, sun kai wa wani mutum mai suna Abubakar, wanda aka ɓoye sauran sunansa, hari tare da soka masa makami, lamarin da ya haddasa karaya a hannunsa na hagu da ƙafarsa ta hagu, baya ga wasu raunuka a sassa daban-daban na jikinsa.
Ɗansa mai shekaru 30 shi ma ya samu raunuka, yayin da aka lalata babura biyu mallakar iyalinsa.
Binciken farko ya nuna cewa harin ya samo asali ne daga rasuwar wani Halilu Ahmad, namiji mai shekaru 20, wanda ya rasu a ranar 16 ga Oktoba, 2026. Ana zargin waɗanda suka kai harin sun danganta mutuwarsa da maita ko tsafi da suka yi zargin ɗan wanda aka kai wa harin ne yake aikatawa.
Bayan faruwar lamarin, jami’an bincike na sashen ’yan sanda na Alkaleri sun gudanar da bincike cikin sirri, inda da misalin ƙarfe uku na rana a ranar 18 ga Oktoba, 2026, suka kama waɗanda ake zargi su goma sha bakwai tare da kai su hedikwatar sashen.
Dukkan waɗanda aka kama maza ne daga ƙauyen Gobirawa, kuma sun haɗa da:
Dayyabu Umar, mai shekaru 18.
Malam Sule Muhammadu, mai shekaru 50.
Usman Dabo, mai shekaru 20.
Umar Suleiman, mai shekaru 22.
Aminu Ahmad, mai shekaru 18.
Bello Umar, mai shekaru 20.
Sani Ibrahim, mai shekaru 18.
Abubakar Ayuba, mai shekaru 25.
Auwal Abdullahi, mai shekaru 22.
Ayuba Ahmad, mai shekaru 30.
Halilu Ahmad, mai shekaru 22.
Umar Rabi’u, mai shekaru 18.
Dauda Rabi’u, mai shekaru 20.
Ashiru Alh. Abdulkarim, mai shekaru 20.
Abubakar Lamiru, mai shekaru 25.
Adamu Ibrahim, mai shekaru 22.
Bashiru Rabi’u, mai shekaru 20.
A halin da ake ciki, sakamakon tabarbarewar lafiyar wanda aka kai wa harin, an fara kai shi Babban Asibitin Alkaleri, daga bisani kuma aka tura shi Asibitin Ihsan da ke Bauchi domin samun ƙarin kulawa ta likitoci, yayin da lamarin ya ƙara tsananta saboda zargin yunƙurin kisan kai.
Saboda haka, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, mni, psc(+), ya bayar da umarnin miƙa shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jiha (SCID), Bauchi, domin gudanar da cikakken bincike, kama waɗanda suka tsere da kuma tabbatar da gurfanar da duk waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sandan ya nuna rashin amincewarsa da ɗaukar doka a hannu bisa zarge-zargen camfi da ba a tabbatar da su ba. Ya gargaɗi jama’a cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani aiki da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da bin doka da oda ba.
Ya kuma tabbatar wa waɗanda abin ya shafa da sauran jama’a cewa za a tabbatar da adalci.
A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wata matsala ko saɓani ga hukumomin tsaro domin a bi hanyoyin da doka ta tanada, maimakon ɗaukar doka a hannu.


