Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
Published: May 18, 2026 at 7:20 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: May 18, 2026

Jam’iyyar APC ta fitar da ɗan takararta na kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya mai ƙunshe da ƙananan hukumomin Akko da Yamaltu-Deba bayan gudanar da zaɓen fidda gwani cikin lumana tare da halartar dimbin magoya bayan jam’iyyar.

Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana a jihar Gombe, Aliyu Gerengi daga ya ruwaito cewa, bayan kammala zaɓen, jami’in da ya jagoranci zaɓen, Dr. Habu Dahiru, ya bayyana sakamakon a garin Kumo inda ya ayyana tsohon Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Mohammed Ahmadu Jarman Deba, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Dr. Habu Dahiru ya ce an tantance masu kaɗa ƙuri’a dubu 53 da 310, inda DCP Mohammed Ahmadu ya samu ƙuri’u dubu 42 da 785, lamarin da ya ba shi nasara a kan Sanata mai ci, Muhammad Danjuma Goje, wanda ya samu ƙuri’u dubu 10 da 425.

Da yake jawabi bayan kammala zaɓen, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Akko, Usman Bello Kumo, ya bayyana zaɓen a matsayin wanda aka gudanar cikin adalci da lumana.

Ya yaba wa masu zaɓe bisa abin da ya kira kyakkyawan zaɓi tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da nuna irin wannan hali a zaɓukan da za su biyo baya.

Usman Bello Kumo ya kuma yi kira ga al’umma da su mara wa dukkan ‘yan takarar APC baya a babban zaɓe mai zuwa domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa masu ɗorewa.

A nasa jawabin karɓar nasara, tsohon DCP Mohammed Ahmadu ya gode wa duk waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen samun nasararsa tare da alƙawarin ba zai ba su kunya ba. Haka kuma ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da daidaito da ya bai wa kowa dama wajen gudanar da zaɓen fidda gwani cikin nasara a faɗin jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
Next Post: Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito

Karin Labarai Masu Alaka

Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
An Watse A Tattaunawar Tsakanin Rasha Da Ukraine Batare Da Cimma Matsaya Ba Labarai
Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Malaman Makaranta A Tilabery Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
  • Fadar Sarkin Musulmi: Talata Ne 1 Ga Watan Sha’aban Na 1447AH Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya mika sunayen Sabbin Shugabannin NMDPRA da NUPRC Bayan Murabus Din Farouk Ahmad Da Gbenga Komolafe Najeriya
  • Kasar Chadi Ta Rufe Iyakar Ta Da Kasar Sudan Afrika
  • Hukumar Hasashen Kasuwanci Na Zargin Saida Bayanan Sirri Amurka
  • Tashoshin Mai Basa Iya Loda Mai A Rasha Labarai
  • Gwamnatin Tinubu Ta Warware Basussukan Fansho Na Shekaru 18 Afrika
  • Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.