Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata Afrika
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno Amurka
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika

Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco
Published: December 15, 2025 at 9:14 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sanyi mai tsanani ya kase wasu bakin haure ‘yan Afirka a kusa da bakin iyakar Morocco da Aljeriya.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a kasar dake Afirka ta Arewa sun bayyana wannan a matsayin babban abin damuwa kuma abinda ya keta ‘yancin zirga-zirgar murtane.

Wata gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil Adama a kasar Morocco, ta ce an gano gawarwakin maza 7 da mata biyu a yankin Ras Afour mai tsaunuka, inda sanyin hunturu yake yayi tsanani sosai.

Kungiyar ta ce wadannan bakin haure ‘yan gudun hijira sun mutu a sanadiyyar sanyi mai tsanani wanda jikinsu dake gajiye ba zai iya dauka ba.

An ce daya daga cikin ‘yan gudun hijirar dan kasar Guinea ne.

A duk shekara, dubban ‘yan Afirka dake kwadayin zuwa kasashen turai su na bi ta cikin hamadar Sahara zuwa kasashen Afirka ta yamma daga inda suke fatan tsallakawa zuwa turai, amma irin wannan balaguro yana da tsananin hadari, kuma daruruwa suna mutuwa ba tare da sun kai inda suke son zuwa ba.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO
Next Post: Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
Kasar Iran Zata Kai Hare Haren Ramuwar Gayya Isra’ila Afrika
Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
UPF Ta Bukaci Haɗin Gwiwa Da NERDC Domin Gina Al’umma Mai Zaman Lafiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata
  • NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
  • Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Zata Raba Taki Ga Manoma Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Game Da Matsalar Tsaro A Najeriya Najeriya
  • Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani Najeriya
  • Ukraine Ta Tura Tawagar Kwarerru Zuwa Kasashen Larabawan Domin Basu Kariya Labarai
  • Tinubu: Abba Magajin Aminu Kano Ne A Fagen Siyasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.