Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Bukaci Al’ummar Gombe Su Haɗa Kai Wajen Yaƙi Da Ta’addanci
Published: June 29, 2026 at 10:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jawabin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan-Majen Gombe), kan Gangamin “Hada Kai Domin Yaki da Ta’addanci”

Yau Litinin, 29 ga Yuni, 2026
Ya ku al’ummar Jihar Gombe masu daraja,
Ina yi muku wannan jawabi ne cikin nauyin alhakin da ya rataya a wuyana da kuma kudurin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban jiharmu da kasarmu baki daya. Yayin da muke ci gaba da samun nasarori wajen gina al’umma mai zaman lafiya da walwala, yana da muhimmanci mu kasance masu hadin kai da jajircewa wajen yakar ta’addanci da sauran nau’o’in laifuffuka.

Tsaro da jin dadin jama’armu dole ne su kasance fifikonmu gaba daya, kuma tare za mu kara karfafa kudurin kare al’ummominmu da kuma kiyaye zaman lafiyar da muke alfahari da shi.

Shekaru da dama kenan da kasarmu, musamman yankin Arewa maso Gabas, ke fuskantar kalubalen tsaro da suka gwada juriyarmu da karfin zuciyarmu.

Ina mai jaddada cewa rashin tsaro shi ne babbar barazana ga zaman lafiya da ci gaban Arewacin Najeriya. Akwai alaka kai tsaye tsakanin tsaro da ci gaba. Ba za a samu ci gaba ba tare da tsaro, haka kuma ba za a samu zaman lafiya mai dorewa ba tare da ci gaba. Wadannan ginshikai biyu suna tafiya tare, kuma dole ne mu ba su kulawa iri daya.

Ina yaba wa jajirtattun jami’an tsaro na rundunar sojojin Najeriya, rundunar ‘yan sanda, Hukumar DSS, NSCDC da sauran hukumomin tsaro bisa sadaukarwar da suke yi. Dare da rana suna tsaye suna kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Muna girmama jarumtakar su tare da tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikinsu. Hakika muna bin su da iyalansu bashin godiya mai girma.

Duk da cewa Jihar Gombe tana cikin yankin da ke fuskantar matsalolin tsaro a Arewa maso Gabas, jihar ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali.

Wannan ba kwatsam ba ne, sakamakon manufofi ne na musamman, zuba jari a harkar tsaro da kuma hadin kan jama’a.
Tun bayan hawana mulki a shekarar 2019, gwamnatinmu ta dauki matakai masu muhimmanci wajen karfafa tsarin tsaro.

Mun kafa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, mun samar da Hukumar GOSTEC domin taimaka wa jami’an tsaro, sannan muka kafa Operation Hattara, wani hadadden tsari na hukumomin tsaro wanda ya inganta saurin mayar da martani ga barazanar tsaro.

Haka kuma mun karfafa kungiyoyin sa-kai na tsaro, mun samar da motocin aiki da sauran kayan tallafi ga hukumomin tsaro, tare da kafa kwamitocin zaman lafiya domin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma sauran sabanin al’umma kafin su rikide zuwa manyan matsaloli.

Mun gudanar da tarukan tsaro guda biyu da suka hada jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da masana. Shawarwarin da aka bayar sun taimaka wajen tsara manufofin tsaronmu, wanda ya haifar da ingantaccen musayar bayanan sirri, saurin daukar mataki da kuma karin hadin kai tsakanin gwamnati da jama’a. Wadannan nasarori ne suka taimaka wajen sanya Gombe cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.

A matsayina na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, tsaro ya kasance a sahun gaba na manufofinmu. Na jagoranci kokarin kafa Asusun Tallafawa Tsaron Jihohin Arewa domin hada karfi da karfe wajen tinkarar matsalolin tsaro da muke fuskanta. Saboda iyakokin jihohi ba sa hana masu aikata laifi motsi, babu jihar da za ta iya magance matsalolin tsaro ita kadai.

Ina kuma yaba wa sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kungiyoyin al’umma, kungiyoyin mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ku ne idanu da kunnuwan al’umma, kuma gudummawarku tana da matukar muhimmanci.
Ga daukacin jama’a kuwa, ina cewa tsaro hakkin kowa ne.

Gwamnati da jami’an tsaro ba za su iya yin wannan aiki su kadai ba. Ina kira ga kowa ya kasance mai lura da abin da ke faruwa a muhallinsa. Idan ka ga wani abu da bai dace ba, ka sanar. Idan ka lura da motsi ko taro ko wani abu da zai iya barazana ga tsaro, ka gaggauta kai rahoto ga hukumomin tsaro.

Bayanan sirri masu inganci suna daga cikin manyan hanyoyin hana aikata laifi da kare rayuka da dukiyoyi.
Ina kuma kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da sabunta dabarunsu domin fuskantar sabbin kalubale. Su hada amfani da fasahohin zamani da kuma dabarun gargajiya, tare da tabbatar da mutunta hakkin dan Adam da gudanar da ayyukansu bisa sahihan bayanan sirri.

Mu ci gaba da yin watsi da ta’addanci, laifuffuka, kiyayya da tashin hankali. Mu karfafa zaman lafiya, hakuri, mutunta juna da fahimtar juna ba tare da la’akari da bambance-bambancen kabila, addini ko siyasa ba. Masu aikata laifi suna samun karfi ne idan akwai rarrabuwar kawuna, amma suna kasa idan al’umma ta hada kai.

Yayin da Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ke ci gaba da daukar matakan magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan, ya zama wajibi al’ummar Jihar Gombe su mara wa wadannan kokari baya.

Ta hanyar hadin kai da jami’an tsaro da kuma kasancewa tsintsiya madaurinki daya, za mu taimaka wajen cimma nasarar yakin da ake yi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.

A karshe, ina kira ga dukkan mazauna Jihar Gombe da su rungumi manufar gangamin “Hada Kai Domin Yaki da Ta’addanci.” Mu tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da duk wani nau’in laifi. Mu tallafa wa jami’an tsaro, mu kare al’ummominmu, kuma mu hada hannu wajen gina Gombe da Najeriya mai zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

Ina addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da kare Jihar Gombe, Ya shiryar da shugabanninmu, Ya karfafa jami’an tsaro, kuma Ya albarkaci Tarayyar Najeriya da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa.

Na gode da sauraron wannan jawabi. Allah Ya albarkaci ku baki daya. Allah Ya albarkaci Jihar Gombe. Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG
Next Post: An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Tare Da Kira Zuwa Ga Kishin Kasa Afrika
Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Bude Kamfanin Sarrafa Ma’adanai A Kasar Mozambique Labarai
Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
  • Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
  • Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • Rikicin Siyasa A Jihar Rivers Sakamakon Ayyana Fubara A Matsayin Shugaban APC Siyasa
  • Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
  • Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.