Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Bude Kamfanin Sarrafa Ma’adanai A Kasar Mozambique
Published: January 31, 2026 at 7:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban kasar Mozambique Daniel Chapo, yayi bikin bude kamfanin sarrafa ma’adinai da ake kira graphite da turanci, wanda zai rika samar da ma’adanai ton dubu metan a shekara, a wani wurin hakar ma’adinai na wani kamfanin kasar China. Anyi bikin ne ranar jumma’a yunkurin kasar na fadada hakar ma’adinai da ake amfani da su wajen hada batura.

Hukumar kula da albarkatun karkashin kasa ta Amurka, ta ce ana tonan wannan ma’adanai ton milyan daya da dubu dari shida a fadin duniya a duk shekara, kuma Mozambique tana daga manyan kasashe da Allah ya yi wa albarkar wannan ma’danai wanda ake amfani dashi wajen hada baturan motoci da basa aiki da mai, da kuma na woyoyin selula.

A jawabinsa wajen bikin shugaba Chapo, yace “Yau muna shiga taswirar masana’antu a duniya, “yanzu mu ba kawai muna samar da kayayyaki da masana’antu suke sarrafawa ba, amma har hakowa da sarrafawa, sannan mu kai shi ketare.”

Kamfanin na kasar China DH Mining, wanda ya fara aikin hakar ma’adanan tun a shekara ta 2014, a kasar, yace ya zuba jarin fiye da dala milyan 200 a wannan fanni. Ya samarda ayyukan yi ga mutane 890 kuma zai karu zuwa 2000.

China ce take da mafi yawan wannan ma’adanai da aka sarrafa a duniya, kuma ta mamaye aikin hakowa da kuma sarrafa shi.

Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 35 A Jihar Borno
Next Post: Shugaban Kasar Tunisiya Ya Tsawaita Dokar Da Baci A Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
Jakadan Amurka A Poland Ya Yanke Hulda Da Kakakin Majalisar Kasar Labarai
Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
  • Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
  • Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
  • Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya Afrika
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • FIFA Ta Buɗe Bincike Kan Koci Hossam Hassan Na Masar Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.