Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika

Mohammed Abdullahi Abubakar Ya Sayi fom Don Tsayawa Takarar kujeran Gwamnan Bauchi A APC 2027
Published: April 30, 2026 at 6:51 PM | By: Bala Hassan

2027: Tsohon Gwamnan Bauchi, da ke Najeriya ya sayi takardan cikewa don yin takarar gwamna a APC

Daga Ahmad Muhammad, Bauchi

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya sayi takardan cikewa ɗin nuna sha’awa da tsayawa takara na muqamin Gwamna a Jam’iyyar APC don tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaven 2027..

Dan takarar Abubakar ya ce matakin ya nuna jajircewarsa ga tsarin da jam’iyyar ta shimfida da kuma ƙa’idodin dimokuraɗiyya na cikin gida.

Abubakar ya ce: “Wannan matakin yana nuna bin ka’ida da na yi wa tsarin jam’iyyar da aka kafa da kuma imanina mara yankewa game da tsarin dimokuradiyya na cikin gida na APC.

“Kamar yadda yawancin masu ruwa da tsaki na APC suka ce, ina sake nanata cikakken goyon bayana ga matsayin jam’iyyar kan amincewa da ko dai kuri’un da aka kaxa ko kuma na zaven fidda gwani kai tsaye, amma saboda hanyar data fi shine idan aka samu daidaito aka cimma matsaya wajen zavar ‘xan takarar gwamna, zai taimaka wajen inganta hadin kan cikin gida, rage tsadar kashe kuxi wajen zaven fidda Gwani,da qalubalen dabaru na zaben fidda gwani kai tsaye, da kuma rage barazanar rashin gaisuwa, da kai qara da shari’a da sauya sheqa daga masu neman takara da suka fusata saboda yana samar da “’yan takara masu dacewa ta hanyar daidaita ra’ayin jama’a,

Ya yi kira ga masu fafatawa da su haxu su amince da mutum daya, jam’iyyar da nufin neman hana rabuwar kawuna bayan zaven fidda gwani, tare da tabbatar da hadin kan jam’iyya kamar yadda mafi yawansu suka nuna sha’awa.

“Ina da yaqinin cewa wannan hanyar za ta kara zurfafa dimokuradiyya ta qarfafa hadin kan jam’iyya, da kuma bai wa kowane memba damar jin cewa shi ne wanda ya tsaida xan takarar a lokacin fitowar ‘yan takara,” in ji shi.

Ya kuma sake nanata amincinsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma shugabancin jam’iyyar a matakin qasa da jiha.

“Ina sake nanata girmamawata, biyayyata, da kuma jajircewara mara yankewa ga Shugaban Jam’iyyar APC na qasa kuma Shugaba Bola Tinubu.

“Haka nan ina mika gaisuwata ga shugabannin jam’iyyar a Jihar Bauchi, manyan dattawanta, da dukkan shugabannin da aka san su waɗanda jagorancinsu ke ci gaba da tsara manufofin ci gaba na APC,” in ji shi.

Dan takarar gwamna ya yaba wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da magoya bayansu saboda goyon bayansu kuma ya yi alƙawarin aiwatar da ayyukan da Zai kyautata rayuwar al’umma Idan yayi nasarar zaɓensa a matsayin Gwamnan Jihar na gaba.

Abubakar ya kammala wa’adinsa na farko kuma ya sha kaye a zaɓen a 2019, yanzu yana son dawowa don kammala wa’adinsa na biyu na zaɓe.

Yawan ‘yan takarar da suka sayi tikitin takarar Gwamna na APC daga Bauchi yanzu su ne Shehu Buba , Yusuf Tuggar, da tsohon Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar. Sauran waxanda Basu saya ba ana Ganin akwai Ministan lafiya Ali Pate, Dokta Bala Wunti DA Nura Many Soro zuwa lokacin da muke haxa wannan rahoto

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Bukaci Samar Da Zaman Lafiya A Filato
Next Post: ‘Yan Sanda A Jihar Gombe Sun Karyata Kona Gidan Nafiu Bala

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya Afrika
Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe
  • Ana Cigaba Da Shirye-Shiryen Fara Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Sabbin Dakunan Karatun Dalibai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas Labarai
  • Jagoran Kasar Iran Yace Basa Bukatar Tallafin Kasar Amurka Afrika
  • Hawan Sallah A Jihar Katsina Afrika
  • Masar Ta Jibge Jiragen Yaki Marasa Matuka Afrika
  • Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
  • Chelle: Rashin Jituwa Tsakanin Osimhen Da Lookman Matsala Ce Ta Cikin Gida Wasanni
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.