Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
  • Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026 Afrika
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola Afrika
  • ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika

Gwamnatin Gombe Ta Dauki Sabbin Matakan Tsaro
Published: January 5, 2026 at 8:07 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta ɗauki wassu sabin matakan tsaro masu ƙarfi don ƙarfafawa da inganta tsaro a faɗin jihar.

Babban Lauyan Gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a Barista Zubairu Muhammad Umar ne ya sanar da waɗannan matakai jim kaɗan bayan da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranci babban taron Majalisar Tsaro don duba ƙalubalen tsaron dake tasowa da kuma abubuwan da suka faru kwanan nan a jihar.

Barista Zubairu Umar yace bayan cikakken nazari kan rahotannin ɓarnata ababen more rayuwa da aikata laifuka masu alaƙa da haka, Majalisar Tsaron ta amince da haramta sana’ar Bola Jari nan take, tana mai nuni da manyan barazanar tsaro dake tattare da sana’ar.

Majalisar ta nuna matuƙar damuwa game da yadda ake ci gaba da lalata kayayyakin more rayuwa a makarantu da sauran kadarorin gwamnati, waɗanda galibi a ƙarshe suke shiga hannun dillalan ƙarafan na Bola Jari.

Yace da dama daga cikin masu gudanar da sanar ba su da tsari ko jagorancin da aka amince da shi, da kuma dokokin dake daidaita sana’ar, wanda hakan ya sa harkokinsu ke da wuyar sha’ani da sanya ido yadda ya kamata.

“Saboda waɗannan matsaloli, Majalisar ta dakatar da duk harkokin Bola jari a faɗin jihar nan take, kuma wannan haramcin zai ci gaba da aiki har sai dillalan sana’ar sun tsara kansu yadda ya kamata a ƙarƙashin shugabancin da aka amince da shi, bayan haka gwamnati za ta samar da cibiyar tattara Bola Jari da za ta riƙa gudana ƙarƙashin kulawar tsattsauran tsaro,” in ji Kwamishinan.

Da yake tsokaci kan sha’anin tsaro a jihar, Barista Zubairu yace Majalisar ta yanke shawarar ƙara himma wajen sanya ido da nazari kan harkokin tsaro, musamman game da mutanen dake ƙaurowa zuwa jihar.

Yace duk mutanen dake son zama ko neman gidajen haya a jihar Gombe ya zama wajibi a tantancesu yadda ya kamata, tare da taskance dukkanin bayanan su don ƙarfafa tattara bayanan sirri da baiwa hukumomin tsaro damar tantance duk mutanen dake jihar idan buƙatar hakan ta kama.

“Duk wanda ya shigo jihar Gombe don zama ko neman hayar gida, dole ne a taskance bayanansa yadda ya kamata hakan zai baiwa hukumomin tsaro damar bibiyar waɗannan bayanai a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso,” in ji shi, yana mai cewa an ɗauki wannan mataki ne don daƙile aikata laifuka da kuma inganta tsaro.

Dangane da rikicin manoma da makiyaya da ake ci gaba da samu, Babban Lauyan Gwamnatin ya bayyana cewa gwamnati ta kafa kwamitin aiki da cikawa don aiwatar da shawarwarin dake cikin rahoton farko kan gandun kiwo da burtalolin shanu.

Rahoton ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin ya gabatar ne ƙarƙashin jagorancin Tsohon Mataimakin Sifeto Janar na ‘Yan Sanda, AIG Zubairu Mu’azu (Mai Ritaya), wanda ya sake duba gandun kiwo da burtalolin shanu a faɗin jihar.

“Kwamitin aiwatar da dokar zai tabbatar da cewa an ƙwato duk gandun kiwo da burtalolin shanun da aka yi wa kutse,” in ji Barista Zubair Umar.

Ya jaddada cewa an ɗauki matakan ne don inganta zaman lafiya da ƙarfafa tsaro da kuma inganta tattara bayanan sirri daga tushe.

Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmad Chuso, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi bayan sace-sacen mutane da kashe kashe da aka yi kwanan nan a Pindiga dake Ƙaramar Hukumar Akko.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya tabbatarwa mazauna yankin cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sacen, da kamo waɗanda suka aikata laifin don magance sake afkuwar hakan.

‘Yan sanda tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, suna bin diddigin waɗanda suka aikata laifin kuma za su tabbatar cewa an ceto waɗanda aka sacen ba tare da wata matsala ba, yace Gwamna ya bada umarnin a gabatar da rahoto kan binciken da muka gudanar ya zuwa yanzu, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin doka,” in ji CP Chuso.

Hakazalika, Mai Martaba Sarkin Yamaltu, Alhaji Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa Majalisar Tsaron ta yanke shawarar ƙara ƙarfafa tsarin tsaron jihar a matakin ƙananan hukumomi ta hanyar amfani da ƙungiyoyin ‘yan banga da mafarauta don ƙarfafawa hukumomin tsaro na yau da kullum tare da hadin gwiwa.

A cewarsa, matakin zai inganta sanya ido kan al’umma da hanzarta ɗaukan mataki ga duk wata barazanar tsaro.

“Waɗannan ‘yan banga da mafarauta za su yi aiki tare da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cikakken sanya ido da tsaro a faɗin jihar,” in ji Sarkin.

Gwamnan ya kuma umarci Shugabannin Kananan Hukumomi da Sarakunan Gargajiya su ci gaba da gudanar da tarurrukan bitar sha’anin tsaro na mako-mako a matakin ƙananan hukumomi don tantance lamuran dake faruwa da kuma ɗaukar matakan kariya don tabbatar da tsaro da kare al’ummar jihar.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe
Next Post: An Hana Yada Rahotannin Siyasa A Kasar Uganda

Karin Labarai Masu Alaka

Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
Najeriya Da Amurka Sun Karfafa Alakar Tsaro Afrika
Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar
  • Sakon Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu A Ranar Dimokraɗiyya Ta 2026
  • Za’a Bude Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Ta Duniya 2026
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup
  • Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Akan Cutar Ebola

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kashe Sojojin Ukraine Dubu 55 A Kasar Rasha Afrika
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
  • Najeriya: Ta Aiwatar Da Tsarin Ba Aiki Ba Albashi Ga Ma’aikata Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.